Kuɗin fim a Nollywood ba ɗaya ne da na Kannywood ba – Abba Zaky 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Sadiƙ Ali Zaky, wanda aka fi sani da Abba Zaky, fitaccen jarumi ne da ke taka rawa masana’antar fim ta Nollywood da Kannywood, a tattaunawarsa da Ibrahim Hamisu a Kano za ku ji yadda ya fara da fim ɗin da aka nuna shi a babbar manhajar nuna finafinai ta duniya wato Netfliɗ, za ku ji tarihinsa da kuma bambancin da ke akwai tsakanin finafinan Nollywood da na Kannywood, ku biyo mu:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar da kanka.

ABBA ZAKY: Sunana Sadiƙ Ali Zaky amma anfi sani na da Abba Zaky. 

Wane ne Abba Zaki?

An haife ni a Gyadi-Gyadi Kano, na yi primary da secondary school a Kano. Na yi university a Gombe State University inda na yi degree na a Islamic Studies. Na yi NYSC a Benue 2015.

Ta yaya aka samu kai a fagen finafinai?

Da yake tun da na taso nake da baiwar rubutun waƙoƙi tun 2005 na fara zuwa studio in buga waƙa. To har na je university ina yin waƙoƙi har album na yi. Amma bayan na yi NYSC sai kuma na fara alaƙa da ‘yan fim da haka ni ma na ji na fara sha’awar acting. Amma ban fara shiga fim ba sai 2017.

Me ya baka sha’awa ka shiga harkar fim?

Na daɗe ‘actors’ suna burge ni gaskiya amma ban taɓa tunanin zan yi fim ba sai da abun yazo.

Da wane fim ka fara?

Na fara da wani Nollywood fim mai suna ‘Voiceless’ a 2017.

Sannan akwai ‘Akwati’, ‘Jaru Road’, ‘The Herd’, Hussain( short film), Blood Of Enogie (Series), da sauransu. 

Ko za ka lissafa mana wasu daga cikin finafinan ka a Kannywood?

A Kannywood akwai: Nanjala, Princess Of Galma, In Search Of The King, Lulu Da Andalu, Mashahuri, Gidan Danja, Alaƙa.

Kawai sai aka ganka a finafinan kudu me ya kai ka can ?

Eh ai ni dama fim ɗina na farko ma na Kudu ne ba na Arewa ba. Shiyasa ma za a ga fina-finai na Kudu sun fi yawa a kan na Arewa. 

To yaya za ka kwatanta finafinan Kannywood da Nollywood?

Eh to ai bambanci a fili yake saboda Nollywood kuɗin da suke zubawa su yi fim ba ɗaya ba ne da wanda ake zubawa a Kannywood. Kasuwar da fina-finan Kudu suke da ita babu ita a Kannywood saboda bama yin ayyukan da za su samu shiga a manyan kasuwannin fim. Mu Kannywood yanzu bamu da wata kasuwa da ta wuce youtube saboda babu sinimomi a Arewa. Guda ɗayan da ake da ita a Kano ma, Filmhouse Cinema, ta tashi. Kowa ya koma YouTube inda bai wuce a samu kuɗin cefane ba nan ɗin ma in ka duba za ka ga duk an fara yin yawa tarkace ya yawaita a kai. 

Dangane da waƙa fa yaushe ka fara waƙa?

Tun 2006 na fara waƙa kuma ko last 2 years na yi waƙa inaga shi ne last time da na yi waƙa tare da wani abokina mawaƙi Phaysal Othman.

Ya zuwa yanzu waƙoƙi nawa ka yi?

Na yi waƙoƙi da yawa gaskiya. In za a haɗa da nawa na kaina da kuma na aure da na suna da naɗin sarauta da na gwamnoni da na yi sun kai 200 ko, ga kaɗan daga ciki: 

Ya Allah, Yafe Binta, Dokar Daji, Gwauron, Zance, Sindarin So, Duniya Majingina, da kuma Islam.

Shin yanzu ka daina waƙar ne?

Ba wai na daina waƙa ba ne ‘completely’ amma ka san a rayuwa in kaga abunda ya fi karɓar ka sai kaima ka karɓe shi. Fim ya fi karɓa ta a kan waƙar ne shiyasa ma mutane ba su son ina waƙa ba. Amma still zan cigaba da yi koda sama sama ne.

Waɗannan irin nasarori za ka iya cewa ka samu daga lokacin da ka fara zuwa yanzu?

Eh gaskiya dai daidai gwargwado na samu nasarori saboda ace na fara fim da Nollywood kuma shi ɗin ma ya hau kan Netfliɗ sannan sunana ya shiga cikin IMDB wanda duk wani jarumin fim da ya isa a duniya sunansa yana wajen. Sannan fim ɗin da na yi ‘Voiceless’ ya samu nasarori da lambar yabo a ƙasashen waje da nan gida Nijeriya.

ƙalubale fa akwai ko babu?

E ƙalubane da akwai shi kam saboda gaskiya a Kannywood ba a kira na aiki saboda bana cikin wata da’ira ta jarumai da ake aiki da su. Akwai furodusoshin da akwai jaruman da suke aiki dasu kuma kowanne fim su zasu saka ko sun dace ko ba su dace ba. To amma hakan sai ya zama ya buɗe min wata ƙofa da kuma ake kira na aiki a Nollywood saboda su sun yarda na iya kuma suna bani manyan ayyuka.

Wane ne maigidanka a Kannywood?

E to maigida ya danganta da a wane fanni ake magana. Ina da masu gida a Kannywood wanda suka taimake ni ta fannin rayuwa da shawarwari kamar Ali Nuhu sai kuma wanda suka taimake ni ta fannin sana’a ta fim su ne Prince Daniel Aboki, Kabiru Jammaje da Yakubu Muhammed wanda su ne suka ba ni dama suka ba ni roles ɗin da za su taimake ni a matsayin actor. 

Wane fim ne ba za ka taɓa mantawa da shi ba saboda irin ƙwazon da ka yi ko wahalar da ka sha?

Gaskiya fnafinai ne guda biyu wanda bazan manta da su ba nan kusa ɗayan saboda na nuna ƙwazo na a matsayina na ‘actor’ kuma na saka kaina a cikin hatsari sosai saboda in bada abunda ake so. Fim na farko shi ne ‘Akwati’ wanda Prince Daniel Aboki ya shirya wanda muka ɗauka a Kaduna. Na biyu kuma shi ne ‘Jaru Road’ wanda Kenneth Gyang ya shirya wanda muka ɗauka a Jos. Na sha wahala sosai a ayyukan fim ɗin nan kuma ban taɓa nuna ƙwazo a fim kamar su ba gaskiya.

Mene ne burinki a nan gaba?

Burina shi ne ace wani casting a director a Hollywood ya ganni ya sakani a cikin wani fim din Hollywood ni shi ne babban burina a wannan sana’a gaskiya. Saboda ba Nollywood ba ne target ɗina chan sama nake burin tsallakawa. 

Ƴan matanka nawa?

Budurwata guda ɗsya ce. Ni ba na tara ƴammata. Shiyasa tunda aka ƴaudare ni a shekarun baya na ɗau shekaru ban ƙara yin wata budurwar ba. Yanzu ma guda ɗayan ce. 

Yaushe za ka yi aure?

To! ina sa rai nan da shekarar 2027 Insha Allah zan angwance.

By ukarofi