
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ya bayyana damuwarsa game da ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi a kwanan nan, yana mai bayyana hakan a matsayin kira ga ƴan Nijeriya na su farka don ganin sun kare martabar ƙasarsu.
A wata sanarwa ta kafar X a jiya Litinin, Obi ya ce Nijeriya tana fuskantar matsanancin ƙalubalen tsaro da ya tarwatsa rayuka da dukiyoyin al’umma tun daga 2023 zuwa yanzu inda aka rasa rayuka sama da 10,000.
Ya ce, kashe-kashen ba abu ne da za ƙaurace wa ba waɗanda suan faruwa ne sakamakon gazawar gwamnati da rashi shugabanci na gari daga ɓangaren jagororin ƙasar.
Ya bayyana cewa, gwamnan APC ta gaza samun makamaar aiki da kishi wajen ganin ta magance matsalolin ta’addanci da suka jima suna addabar al’umma.
Tsohon gwamnan na Anambra ya kuma yi ƙalubale game da barazanar Amurka ta kawo hari a Nijeriya, yana mai kira ga ƙasashen biyu da su haɗu su yi aiki tare wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci a ƙasar.
