
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An yi zargin wani sojan Nijeriya da cin alwashin fafatawa da sojojin Amurka yayin da Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kai hari Nijeriya bisa ikirarin kisan kiyashin Kiristoci.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, sojan, wanda ya bayyana kansa da suna Soja Boy, ya yaba wa rundunar sojojin Nijeriya inda ya ce sun yi yaƙi a ƙasashen waje yayin da aka gayyace su don haka kada a raina ƙarfinsu.
Ya kuma soki sojojin Amurka da cewa dakarunsu ba za su iya jue wa yanayin Nijeriya ba ta fuskar zafin rana da makamantansa.
Kalaman sojan, wanda ba shi ne matsayar sojojin Nijeriya ba, na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Amurkan ya yi barazanar ɗaukar matakin soja akan Nijeriya.
A ranar Juma’a ne Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta, inda ya ce Kiristoci suna fuskantar matsi da tauye musu ƴancin addini.
Saidai, ikirarin nasa ya samu rashin amincewa daga jama’a da dama a ɓangarorin siyasa, addini da dai sauransu duba da yadda aka yi ta musantawa.
