
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore ya yi watsi da barazanar Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump akan ɗaukar matakin soja a Nijeriya, sakamakon zargin yi wa Kiristoci kisan gilla, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda zai haddasa tashin-tashina acikin al’umma.
A wani rubutu ta Soshiyal Mediya, Sowore ya ƙalubalanci masu murna da matakin, yana mai cewa hakan illa ne da ka iya shafar kowane addini ƙabila a ƙasar.
Ɗan siyasar ya kuma ce samar da mafita game da matsalolin Nijeriya ba abu ne ba za a magance ta tayat da boma-bomai ba, sai dai ɗauki take buƙata da zai bai wa dukkan ƴaƴanta kariya daga ayyukan ta’addanci.
Kazalika, ya ce Shugaban Amurkan bai damu da ƴan Nijeriya ba na kowane ɓangare, yana mai bayyana ceton Nijeriya a matsayin abinda zai samu daga cikinta ba wani ɗauki na ƙasar waje ba.
