
Rundunar ƴan sanda a Jihar Legas, ta ayyana ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sa da tayar da hankalin jama’a da yunƙurin rufe hanyoyi.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mashood Olohundare Jimoh ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya tabbatar da cewa an kama mutum 13 da ake zargi da hannu a cikin tashin hankali da rikicin da ya biyo bayan rushewar gine-gine a yankin Oworonsoki na jihar.
Da yake magana da manema labarai a a gadar ‘Third Mainland Bridge’ da ke Oworonsoki, CP Jimoh ya jaddada cewa rundunar ƴan sanda za ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa babu wanda ya sake ta da hankalin al’umma ko ya barazana ga zaman lafiyarsu a jihar.
A karo na biyu cikin ƙasa da mako guda, kwamishinan ƴan sandan ya tura jami’ai ɗauke da makamai zuwa wurare daban-daban a faɗin jihar domin hana masu zanga-zanga toshe hanyoyi.
A cewar kwamishinan, an tura jami’an tsaro da yawa ba iya yankin Third Mainland Bridge ba, har ma zuwa wasu sassa na jihar, inda ake kyautata zaton za a gudanar da zanga-zanga.
