
Kwamandan sojin da ke mulkin ƙasar Guinea tun bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin da ta gabata a 2021, Kanal Mamadi Doumbouya, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar.
A jiya Litinin, Doumbouya ya je kotun kolin ƙasar sanye da baƙin gilashi tare da rakiyar dakarunsa, inda ya mika takardun neman tsayawa takara ga alƙalan kotun.
Saidai, an hana manyan jam’iyyun adawa na Guinea shiga zaɓen da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa.
A watan da ya gabata ne al’ummar ƙasar suka nuna mamaki bayan da gwamnatin ƙasar ta sanar da cewa duk wanda ke son tsayawa takarar shugaban ƙasa dole ne ya biya kuɗin rajista har kimanin Dalar Amurka 100,000.
