
Tsohon jagoran mayaƙan yankin Neja-Delta, Asari Dokubo, ya gargaɗi Shugaba Donald Trump na Amurka da ya janye barazanarsa ta kai hari kan Nijeriya bisa zargin kashe Kiristoci.
Asari ya ce, Nijeriya ba za ta lamunci kowace irin barazana daga ƙasashen waje ba, musamman wadda ta ke neman lalata martabar ƙasar da tsaro.
Ya yi gargaɗin cewa, duk wani yunƙurin kai hari ga Nijeriya zai zama babban kuskure da ka iya haifar da mummunan sakamako ga Amurka.
A cewarsa, Nijeriya za ta zama mazaɓarta ga Trump da duk wasu sojojin Amurka da za su kuskura su kai harin da yake yi wa ƙasar barazana da shi.
Kazalika, ya yi nuni da cewa al’ummar Nijeriya suna tsayuwa tsayin daka wajen kare ƙasar da mutuncinta a idon duniya.
