
Sanannen Malamin addinin Musuluncin nan a Nijeriya, wato Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa kan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.
Malamin ya yi kiran ne bayan barazanar da Donald Trump ya ya yi na kai farmaki a Nijeriya game da zargin kisan Kiristoci.
Trump ya ba Nijeriya zaɓi da cewa dole ta yi gaggawar kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa ko kuma ya ɗauki matakin soja akanta.
Hakan ya janyo martani da dama daga ɓangarorin kasar yayin da masana ke cewa wannan barazana ba alheri ba ne ga kasar.
Ya bayyana maganganun Trump a matsayin cin mutunci ga ikon Nijeriya da rashin girmamawa ga kasar wanda yunƙuri ne na zubar mata da kima.
A cewarsa, bai kamata gwamnati ta yi shuru ba kan waɗannan kalamai masu tayar da hankali saboda girma da tasirin da za su yi Nijeriya da al’ummarta.
Kazalika, Gumi ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta kira jakadan Amurka domin neman karin bayani da neman janye kalaman, yana mai jan kunne cewa ɗaukar matakin ka iya kai ga yanke hulɗa da gwamnatin Trump.
