Zargin kitsa juyin mulki: Lauyoyi sun shiga bisa tsare ɗan uwan Sylva da direbansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’amarin zargin kifar da gwamnati a Nijeriya na cigaba da samun rashin tabbas yayin da har yanzu ake tsare da mutane biyun da aka kama a samamen gidan tsohon Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva, mako guda da yin atisayen.

Tun a ranar 25 ga watan Oktoba, 2025 ne aka kama Paga Sylva, wanda ƙani ne ga tsohon gwamnan na Bayelsa da mai taimaka masa akan harkokin cikin gida da direbansa.

Saidai, Sylva, wanda jigo ne a jam’iyyar APC kuma ginshiƙi ga siyasar Bayelsa, ba ya ƙasar a lokacin da jami’an suka kai samame a gidan nasa.

Majiyoyin tsaro sun ce da fari ya shirya dawo wa Nijeriya, amma daga bisani ya soke hakan sakamakon jin cewa an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin zargin juyin mulkin.

Mai taimaka masa akan harkar yaɗa labarai, Julius Bokoru ya ce har yanzu ana tsare da mutanen ba tare da gabatar musu da wata hujja da ke alaƙanta su da wani mummunan aiki ba.

Ya kuma soki abinda ya kira da ‘ƙoƙarin dameji ga dukiyar Sylva’ a yayin atisaye, inda ya zargi wasu ƴan siyasa da ƙoƙarin ɓata wa tsohon ministan suna saboda kallonsa a matsayin matsala a gare su.

By Babaji