Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da kasafin kuɗin 2026 a zauren majalisar jihar Katsina.
Ya ce a kasafin kuɗin 2026 an sami ƙarin Naira biliyan 205 idan aka kwatanta da kasafin kuɗi na 2025.
Ya kuma bayyana dalla dalla nasarorin da gwamnatin sa ta samu wajen aiwatar da kasafin kuɗin 2025.
A fannin noma gwamnatin jihar ta samar da buhu 400,000 na takin zamani da aka raba a kowace rumfar zaɓe guda 361 da ke faɗin jihar.
Haka kuma gwamnati ta samar da injinan noman rani da taractoci da horar da malaman aikin noma a cewar gwamnan.
Ya ɗauki tsawon lokaci yana bayyana nasarori akan harkokin Ilmi, kiwon lafiya,tsaro da sauran aikace aikace da gwamnatin sa ta aiwatar ƙarƙashin kasafin kuɗi na 2025.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya yaba da kyakkyacwar dangantaka da ke tsakanin gwamnatin jihar da majalisar dokokin jihar Katsina da ya ce ya taimakawa gwamnatin sa wajen aiwatar da muhimman ayyuka na raya ƙasa.
Yana fatan wannan dangantaka za ta cigaba domin gwamnatin sa ta ƙara aiwatar da muhimman aikace-aikace na raya ƙasa.
A jawabinsa shugaban majalisar Shamsuddeen Abubakar Dabai ya ce gwamna Dikko Raɗɗa ya yi abin a yaba masa dangane da yadda yake jagorancin jihar.
Hon Shamsuddeen ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a wannan shekara wanda yace yafi na shekarar bara.
Daga nan sai kakakin majalisar Hon Nasiru Yahaya Daura da ɗaukacin ‘yan majalisar suka tashi tsaye suka amince da sake takarar Gwamna Dikko Raɗɗa.
