
Hukumar Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta ce abin da ya faru wani ɓangare ne na aikinsu na yau da kullum ba wani kamawa ko tsangwama ba.
Kakakin hukumar, Akinsola Akinlabi ya bayyana cewa an duba fasfon nata ne bisa bin tsarin tsaro da ake aiwatarwa ga dukkan matafiya, musamman manyan jami’an gwamnati da ƴan majalisa.
A cewarsa, “Ba a kama ko ƙwace fasfon Sanata Natasha ba. An yi bincike ne kamar yadda ake yi wa kowa, kuma an mayar mata da takardunta nan take.”
Saidai wasu majiyoyi daga ofishin Sanatar sun bayyana cewa an tsare ta na ɗan lokaci a filin jirgin sama kafin ta cigaba da tafiya, abinda suka ce ya saɓa da mutuncin ofishin Sanatar.
Hukumar ta jaddada cewa tana aiki bisa doka da tsarin tsaro, ba tare da nuna bambanci ba ga kowanne ɗan ƙasa.
Ya ƙara da cewa, Sanatar ta iya watsa batun cewa an karɓe mata fasfo, amma kuma ba ta yi bayani daga bisani ba bayan an ba ta fasfo ɗin nata.
