
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani karo, Gwamnatin Tarayya ta ta yi watsi da ikirarin Gwamnatin Amurka na ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta (CPC) bisa zargin tauye ƴancin addinin wani ɓangare na al’ummar ƙasa, tana mai bayyana hakan a matsayin kuskuren fahimta game da halin tsaro a ƙasar.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, FNIPR, yayin jawabi ga manema labarai a Cibiyar Yaɗa Labarai ta ƙasa da ke Abuja, ya ce matsayar Amurka akan al’amarin abu ne da ke ƙoƙarin raina ɗimbin nasarorin da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi akan yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin ƙwato garuruwa da dama da suka shiga hannun ƴan ta’adda a baya.
Ministan ya kuma yi watsi da batun ɗaukar matakin soja akan Nijeriya na Shugaba Donald Trump, yana mai cewa ire-iren barazanar sun samo asali ne daga rashin fahimtar ainihin halin tsaron Nijeriya.
Ya kuma bada misali da rikicin Boko Haram da ya faɗaɗa tun a shekarar 2009 wanda ya ɗaiɗaita al’ummomin Musulmi da Kirista tare da salwantar da rayukan dubunnan mutane.
Ya bayyana cewa, da dama daga cikin manyan jami’an sojoji da ke sashen leƙen asiri Kiristoci ne da ke aiki kafaɗa-da-kafaɗa da abokan aikinsu Musulmai wajen yaƙar ayyukan ta da ƙayar baya.
Kazalika ya bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi wajen yaƙi da ta’addanci daga 2023 da suka haɗa da hallaka dubunnan ƴan ta’adda da kama sama da guda 13,500.
Haka kuma, an ceto mutane sama da 17,000 da aka yi garkuwa da su da kuma ƴan ta’adda da iyalansu guda 9,800 da suka miƙa wuya.
Ya ƙara da cewa, an ƙwato makamai sama da 124,000 da tarwatsa wasu sama da 11,000, sannan an hallaka jagororin ƴan ta’adda fiye da guda 5,000 da sauransu.
