Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Kusan daga shekaru ashirin da su ka gabata zuwa yanzu, na sha gwagwarmaya da Yan Quraniyyun game da yarda da amfani da hadisi, abinda su ke suka tare da kafa hujjar cewa Qurani kadai ya ishe mu saboda ayoyi irinsu Q6:38 “… Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi (Quran).” Ko Q12:111 “..(Qurani) Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.”
To amma shin, wadannan ayoyi na nufin cewa ba wani abu da za’a iya madogara da shi sai Qurani? Kamar yadda Yan Quraniyyun da duk sauran musulmi su ka yarda cewa babu wani tafsirin Qurani da ya fi inganci irin Tafsir Quran fil Quran, bari mu duba Quranin mu ji karin bayani. Da farko za mu yi karo da ayoyi da dama da ke kira zuwa ga “littafi da hikima”, duk da cewa shi kansa Qurani hikima ce, amma yadda Ayoyin su ka zo, su na raba littafi ne da wata hikima daban, domin a sauran littafai da Allah ya saukar irinsu Attaura da linjila, su ma haka ya kira su, wato “Littafi da hikima”. Kamar yadda Allah ya sanar mana cikin Q4:54 “Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfi da hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.”
Kun ga izina ce cewa ba Qurani kawai Allah ke magana ba a matsayin littafi. Domin kara tantacewar cewa bayan Qurani akwai wasu hanyoyi na shiriya, sai Allah ya ce, Q22:8 “Kuma daga mutãne akwai mai yin musu ga Allah bã da wani
1. ilmi ba
2. Kuma bã da wata shiriya ba
3. Kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba.”
Ka ga a tsanake Allah ya fitar mana da hanyoyi uku na shiriya a wannan aya, wato Ilimi, shiriya da littafi. Ilimi ya kunshi duk wani Ilimi mai amfani da zai amfanar da Dan Adam, kamar kimiyya, falsafa da sauransu. Ita kuma shiriya, akwai abubuwa nagari na gadon al’ada, wadanda kowacce al’umma na da irin nata, da kuma gama-gari wanda ko baka addini ka yarda da su, misali kowa ya yarda a yin gaskiya abu ne mai kyau amma karya babu kyau, ko sata ba kyau ko a wajen barawo ne dss, sannan sai littafan da Allah ya saukar. To ta wadannan hanyoyi Dan Adam zai sami cikakkiyar shiriya wajen rayuwa tagari.
To, idan muka komo kan hadisi kuma, a bayyane ya ke cewa ya fado bangaren Ilimi, kuma zai iya bamu shiriya matukar dai ba karo yayi da Qurani ba. Kuma ko a cikin littafin Musnad na Ahmad Ibn Hanbal, ya ruwaito Annabi na cewa “Duk abinda ya zo muku daga gare ni (hadisi) ku gwada shi da littafin Allah (Qurani), idan yayi daidai da littafin Allah to nine na fada, Amma idan yayi karo da shi, to ba ni na fada ba.”
Kamar yadda kafin wannan hadisin, Allah a cikin Qurani ya umarci Annabi da ya gaya mana cewa, Q10:15 “Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: “Ka zo da wani Alƙur’ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi.” Ka ce: “Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma.”
To, watsi da wadannan tsari da aka yi wajen tantance hadisi shine ya jawo mana rudun da muka sami kanmu a ciki a yanzu. Dalilin da aka sami kafa, tun asali, yadda hadisai da dama su ka kurda cikin littafan hadisi wadanda sun yi karo da koyarwar Qurani da kuma yadda sunnar Annabi ta nuna a zahiri yadda ya rayu. Tarihin yadda manyan maruwaita hadisi su ka yi aikin tantance hadisai kadai, ya isa ya sa mu sha jinin jikinmu. Domin kusan dukkansu, tun daga Imam Malik, zuwa Bukhari da Muslim babu wanda bai yi watsi da kashi sama da 90% na hadisan da ke yawo a zamaninsa ba. Domin idan ka dauki Imam Malik, ya karbo hadisai 100,000 amma ya watsar da 90,000, wato kashi 10% kacal ya aminta da su. Haka nan Bukhari ya karbo 600,000 amma guda 2700 kacal, wato kasa da rabin kashi daya (0.5%) ya iya amincewa ya saka cikin Sahihinsa. Shi kuma Muslim da ya tattaro hadisai 300,000, guda 4000 kacal (kashi 1.3%) ya iya aminta da su.
Wannan matsala ta yawaitar hadisai wadanda manyan maruwaita su ka kaucewa ita ce ta sake haifar da wata matsalar a Ilimin hadisi, wato maida hankali wajen tantance Isnadin hadisi a wancan lokacin fiye da mattaninsa. Ta haka ne kuma abubuwa da su ka ci karo da koyarwar Qurani da yadda Annabi ya rayu, su ka sami kurdawa cikin hadisai.
Bari na bada misali guda daya na irin yadda rashin tantance mattani ya sa wasu abubuwa su ka kurda cikin hadisai wadanda su ka ci karo da koyarwar Qurani. Akwai hadisin da Bukhari da Imam Nawawi su ka ruwaito a matsayin hasan-sahih na “Umirtu an uqatilan nasa” wannan hadisi idan aka tsaya tsai aka yi nazarinsa za’a tarar yayi karo na kai tsaye da ayoyin Qurani da dama irinsu;
“La ikhra fid Deen”
“Imma shakiran wa imma kafura”
“Lakum dinikum wa liyadeen”]
“Fa’abudu ma shi’itum min dunih”
“Fa man sha’a fal yu’imun wa man sha’a fal yakfur” da sauransu.
Sannan kuma yayi karo da tarihin yadda Annabi ya rayu, rabi a Makka da rabi a Madina. Musamman a Madina inda ya sami Iko na mulki amma abinda ya fara gabatarwa da farko-farko shine na samar da yarjejeniyar Madina (Medina Charter) wadda masana tarihi wadanda ba musulmi ba su ka rika yabon cewa ita ce ta farko wadda ta bada damar rayuwa tare da sauran addinai babu tsangwama. Sannan tsawon lokacin da abokan yarjejeniyar su ka cika alkawarin su, an zauna lafiya har sai lokacin da su ka fara karya yarjejeniyar, kuma mun ga yadda Banu Nadir, Banu Qainuqa da Banu Quraiza su ka karya yarjejeniyar a lokuta daban daban, Allah kuma ya umarci Annabi ya watsar da yarjejeniyar.
Sannan ko bayan wafatin sa, cikin shekaru 100 Musulmi su ka mamaye duniyar wancan zamanin, amma duk inda za su yaka sai sun bada zabi uku “Mika wuya, zaman lafiya da biyan jizya, ko yaki.”
Amma sakamakon an tantance wannan hadisi da ga mahangar Isnadi kawai ba tare da la’akari da mattanin ya sami bincikawa a tsanaki ba, sai ga shi ya zama karbabbe yadda kowa ya yarda da sahihancinsa. Shi ya sa, sakamakon na dade ina nazari da bincike a kan kimiyya-addini-falsafa, na gamsu da cewa dole a rika amfani da ma’aunin Qurani, kimiyya da ingantaccen tarihi wajen tantance hadisai. Kuma duk wanda yayi karo da su a ajiye shi a gefe.
Sannan abin la’akari na gaba da zai jaddada haka shine Malaman hadisi sun kasa hadisai zuwa aji-aji, kuma sun yarda cewa hadisi Mutawattir (ko Mashhur), wato wadanda mutane da dama su ka shaida ruwaitarsa, su ne aji mafi inganci a cikin hadisai. A irin wannan aji kuma babu wanda zai hada kafada da hadisin ban kwana wanda a wata ruwayar sahabbai 114,000 su ka halarta. Amma kuma abin da zai ba ka mamaki shine wannan hadisi ya zo da mabanbantan ruwayoyi guda uku, kuma a karshen hadisin banbancin ya bayyana inda ake cewa Annabi yayi wasiyyar bar mana
1. Quran
2. Quran da Sunna
3. Quran da Ahlul Bayt.
To don Allah idan har hadisin da ya fi kowanne shahara da sama da mutane 114,000 su ke a wajen zai zo da banbancin mattani, wanda karara kowa zai gane cewa banbancin aƙida ne ya sami kurdawa cikin hadisin, to ina ga Ahad Hadith wandanda mutum guda ko biyu kacal su ka ruwaito, kuma su ne mafi yawan hadisan?
Kamar yadda na fada a baya, matsalar hadisan karya da marasa inganci ya sa su Bukhari su ka maida hankulansu wajen tantance isnadi, to a yanzu mu kuma tunda ba mu da wannan matsala, kamata yayi mu maida hankali wajen tantance mattani ta hanyoyin Qurani, kimiyya da tarihi. Domin dukkansu babu wanda zai yi karya. Kuma ba sabon abu ba ne kokarin tantance hadisan Sahihain, domin tun a Karni na 10, Al Daraƙutni yayi, kuma a nan kusa ma, Nasiruddeen Albani ya yi.
Matukar ba mu ci gaba da tantance hadisai ba, to hakika hadisai marasa inganci ko wadanda su ka yi karo da koyarwar Allah da manzonsa za su ci ga da kawo mana rikice-rikice da assasa mana banbanci da gaba a tsakanin Musulmi.
Allah ya datar da mu gaba daya.
