
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a Shugaba Bola Tinubu ya yi ganawar da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ne wanda ya yi wa sarkin rakiya yayin zuwansa fadar.
A cewar mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na musamman akan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun wanda ya yaɗa zaman a kafar X, hakan wani ɓangare ne na cigaba da neman shawarwarin jagororin addini da sarakuna akan muhimman al’amuran da suka shafi zaman lafiyar ƙasa.
A farkon makon nan ne Tinubu ya gana da Shugaban ɗarikar Katolika na Abuja, Ignatius Kaigama, yayin da ake fargaba akan ikirarin Shugaba Donald Trump na Amurka cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, lamarin da ya sa ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta.
Haka kuma, Shugaban Amurkan ya yi barazanar ɗaukar matakin soja akan Nijeriya matuƙar aka cigaba da farmakin Kiristoci a ƙasar.
Saidai, Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin inda ta ce al’ummar Musulmi da Kirista suna zaman lafiya tsakanin a ƙasar.
