
Hukumar Kashe Gobara a Kano, ta tabbatar da rasuwar wata tsohuwa mai kimanin shekaru 96, wato Habiba Ado, wacce ta faɗa cikin ramin masai a Kauyen Sarai da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta jihar.
Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce an samu kiran gaggawa daga wani Usman Adamu a ranar Alhamis, bayan gano cewa tsohuwar ta nutse acikin ramin ba-haya.
Akan haka ne jami’an hukumar suke je wajen cikin hanzari, inda suka samu gawar marigayiyar kwance cikin ruwan ramin.
A cewar dangin mamaciyar, Habiba ta dade tana fama da matsalar lalurar ƙwaƙwalwa, kuma sun shafe kwanaki hudu suna neman ta ba tare da samun labarinta ba.
Daga bisani a gano cewa ta faɗa ramin masai inda jami’an hukumar suka fito da gawarta, sannan kuma aka tabbatar da rasuwarta a nan take.
Hukumar ta jajanta wa iyalan marigayiyar, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa sanya ido musamman ga tsofaffi da masu fama da matsalolin lafiya domin kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.
