Kano: Shugaban ƙaramar hukuma ya jajenta rasuwar Alhaji Aminu Bichi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Karamar Hukumar Bichi ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Garba Bichi, wanda ya rasu yana da shekaru sittin a duniya.

Marigayin ya kasance yaya ne ga tsohon Ministan Masana’antu kuma Jagoran Jam’iyyar NNPP, Alhaji Ahmad Garban Bichi.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya bayyana alhininsa game da wannan babban rashi na jigon Jam’iyyar NNPP na karamar hukumar, Garba Bichi suka yi.

Ya kuma yi fatan gafarar Allah ga mamacin da kuma haƙurin jure rashinsa ga iyalansa, ‘yan’uwa, abokan arziki da ma kafatanin danginsa.

Waɗanda suka halarci ta’aziyyar sun haɗa da; Mataimakin shugaban karamar hukuma, Alhaji Abubakar Sulaiman Babangida Danzabuwa, Sakataren Mulki, Hon. Anas Muhammad Abdullahi, Daraktan Mulki, Alhaji Abba Muhammad Diso, Shugaban Kansiloli, Hon. Habibu Musa Fagolo da kuma shugabannin sassa da suka kunshi; na lafiya da ayyukan raya kasa da kuma jin dadi da walwalar jama’a na karamar hukumar.

Su ma sun yi addu’ar samun rahamar Allah ga marigayin da dukkan musulmi da kuma fatan Allah ya bai wa ahalin mamacin hakurin jure wannan rashi, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta bayyana.

By Babaji