Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki sabon mataki na tarihi wajen shata muradunta a fannin samar da lantarki, inda ta amince da shirin mallakar kaso mafi rinjaye na hannun jari a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO).
Wannan mataki, a cewar gwamnatin jihar, zai buɗe sabon babi na ci gaba, musamman wajen inganta wutar lantarki da farfaɗo da masana’antu da harkokin kasuwanci a jihar.
Sanarwar ta fito ne daga kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa karo na 33 a Kano.
A cewar gwamnatin, mallakar KEDCO zai bayar da damar ƙara aarfin jihar wajen samarwa, jigila da rarraba lantarki, lamarin da ke da nufin rage dogaro kacokan ga hukuma ta tarayya da kuma tabbatar da cewa kasuwanci da masana’antu sun samu wutar da ba ta yankewa.
Gwamnatin ta ce, matakin zai taimaka wajen jawo hannun jari daga cikin gida da waje, ƙirƙiro sabbin ayyukan yi, da farfaɗo da masana’antu, musamman a muhimman yankunan masana’antu na Sharada, Bompai da Challawa.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar ta ce ta ƙaddamar da Manufar Wutar Lantarki ta Kano, wadda ke tsara hanyar da za a bi wajen bunƙasa makamashi a jihar, ciki har da amfani da haɗaɗɗun hanyoyin samar da wuta irin su hasken rana (solar).
A wani muhimmiyar ɓangare, majalisar ta amince da gina gidajen low-cost guda 50 a kowace ƙaramar hukuma 36 na jihar, a wajen yankin birane. Wannan shirin, a bayyani, wani ɓangare ne na yunƙurin rage matsalar rashin muhallin iyalai masu ƙaramin yada matsakaicin ƙarfi a jihar.
Gidajen za su zo tare da muhimman ababen more rayuwa irin su hanyoyi, wutar lantarki da ruwa, domin tabbatar da cewa jama’a sun more rayuwa cikin martaba da walwala. Gwamnatin ta ce shirin zai ƙarfafa tattalin arziƙin ƙananan hukumomi, ya samar da ayyukan yi a matakan gine-gine da bayan kammala su, tare da ƙarfafa ci gaban al’umma cikin tsarin zamani.
Da yake ƙarin haske, Sunusi Bature ya ce wannan babban shiri ya nuna jajircewar gwamnatin Abba Kabir Yusuf wajen mayar da Kano cibiyar masana’antu da kasuwanci a arewacin Nijeriya, ta hanyar samar da wuta mai inganci da daƙile matsalar rashin muhalli ta hanyar tsari.
