Akwai darussa da dama da sabbin hafsoshin tsaro za su iya koya daga Janar Musa — APUA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ƙungiyar mai fafutukar haɗin kan Arewacin Nijeriya, ‘Arewa People’s Unity Association’ (APUA), ta yaba wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu bisa naɗa sabon Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, tare da miƙa godiya da jinjina ga tsohon hafsan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, bisa rawar da ya taka wajen kare martabar Nijeriya da inganta tsaro a ƙasar nan.

A taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, Shugaban ƙungiyar APUA na ƙasa, Alhaji Adamu Aliyu, ya bayyana cewa wannan mataki na shugaban ƙasa na jaddada ƙudirin gwamnati wajen ƙarfafa tsare-tsaren tsaro da magance matsalolin da ke addabar ƙasa, musamman a Arewa.

“Mun yaba da hangen nesa da natsuwar Shugaba Bola Ahmad Tinubu wajen zaɓar sabon hafsan tsaro, wanda muke da tabbacin zai kawo sabon kuzari ga rundunar tsaro,” inji Aliyu.

“Haka kuma muna miƙa saƙon girmamawa da godiya ga Janar Christopher Musa kan jajircewarsa da kishin ƙasa a cikin yaƙin da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda da ’yan fashi. Gudunmawarsa ta kasance abin yabo.”

“Muna kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya nemi wani muƙami da zai dace da gogewar Janar Musa ya ba shi, domin ba shi damar ci gaba da amfani da ƙwarewarsa wajen gina ƙasa”

A cewarsa, APUA na fatan sabon hafsan tsaro zai ginu kan abubuwan alheri da aka riga aka cimma, tare da ci gaba da kawowa rundunonin tsaro sauye-sauye masu ma’ana domin ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasa.

ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta ci gaba da bin adalci, cancanta da bin doka wajen naɗe-naɗen manyan hafsoshin tsaro, domin tabbatar da haɗin kai da kwanciyar hankali.

Haka zalika, ta buƙaci Majalisar Dattawa ta ci gaba da taka rawar gani wajen tantance hafsoshi bisa gaskiya da biyayya ga Kundin Tsarin Mulki.

Aliyu ya jaddada muhimmancin tabbatar da wakilci da daidaito tsakanin yankuna wajen jagorancin tsaro, yana mai cewa tsarin tsaron da ya ginu kan gaskiya da amana ne ke gina haɗin kai da amincin al’umma.

Hakazalika, ƙungiyar ta yi kira da a ƙara sa ido kan hukumomin tsaro da na shige da fice, ciki har da hukumar kwastom, domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen gudanar da aiki ga al’ummar ƙasa.

“Mun sadaukar da kanmu ga wanzar da zaman lafiya, hazin kai da adalci. Sauye-sauyen tsaro dole su kasance bisa gaskiya, ɗa’a da manufa ta ƙasa,” inji sanarwar.

A cewar ƙungiyar, Nijeriya ta fi buƙatar haɗin kai da kwanciyar hankali a wannan lokaci fiye da ko yaushe: haɗin kai tsakanin ƙabilu, addinai da yankuna — domin muradun ’yan ƙasa su tabbata. 

Ta kuma jawo hankalin shugabanni su kauce wa siyasantar da tsaro, tare da mayar da hankali kan albarkatun ɗan adam, fasaha da kula da al’umma a ƙauyuka da birane, domin tsaro ya zama gaskiya — ba kawai magana ba.

ƙungiyar ta roƙi ’yan ƙasa su ci gaba da zama masu haƙuri, kishin ƙasa da goyon bayan sahihan manufofi, domin “ƙasa tamu ɗaya ce, kuma tsaron ta na buƙatar gudunmawar kowa.”

By ukarofi