Fim ɗin Kakanda ne gwarzon fim na gasar KILAF Award 2025

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Sakamakon gasar fina-finai ta KILAF AWARD 2025 da aka sanar a daren jiya Asabar 8 ga Nuwamba 2025 an bayyana fim ɗin Kakanda ne ya kasance gwarzon fim na wannan shekarar inda ya yi fice a cikin fina finai masu yawa da suka shiga gasar daga ƙasashe daban daban na duniya da aka yi su da yare da kuma al’adun mutanen Afrika.

Taron wanda aka yi shi a babban ɗakin taro na gidan gwamnatin Jihar Kano mai taken Night Award ya samu halartar manyan mutane daga nan gida Nijeriya da ƙasashe daban daban na Afrika.

Tun da farko da yake jawabin maraba, shugaban gudanar da taron Alhaji Abdulkarem Muhammad ya nuna farin cikin sa ga yadda jama’a suka karɓi taron KILAF AWARD a duk faɗin duniya, wanda hakan ne ya bayar da ƙwarin gwiwar da ya kasance ana yin sa a duk shekara wanda a yanzu ya zama karo na takwad kenan da aka yi shi a jere, don haka muna godiya ga hukumomi da gwamnatin Jihar Kano da ma sauran ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da suke bayar da gudummawar su har taron ya kawo wannan lokacin, kuma muna maraba da dukkan masu taimakawa don ganin wannan taron ya ƙara ci gaba.

Ya ci gaba da cewa “A game da finafinai da suka shiga gasar a wannan shekarar, an samu finafinai 616 wanda a cikin su ne aka fitar da waɗanda suka yi nasara a rukunai daban daban, wanda a yanzu muka taru domin sanar da finafinan da suka yi nasara domin ƙarfafa musu gwiwa da kuma ba su lambar yabo. Muna fatan hakan zai zama hanyar bunƙasar finafinan Afirka da ƙulla alakar kasuwanci da zumunci mai ƙarfi a tsakanin ƙasashen Afrika”.

Bayan kammala jawabin sa ne aka yi wakokin gargajiya na Afirka daga nan kuma aka shiga bayyana sunayen zakarun gasar.

Fim ɗin “Kakanda” shi ne ya lashe kyautuka masu yawa a cikin gasar ta wannan shekarar.
In da ya kasance gwarzon fim da ya yi nasara,
Sai gwarzon jarumi Sadik Sani Sadik da fim ɗin Kakanda, gwarzuwar jaruma Amina Shehu ita ma da fim Kakanda, gwarzuwar mai tallafawa jaruma Ladin Cima da fim ɗin Kakanda.

Gwarzon fim da ya fi nuna al’ada fim din Kakanda. Gwarzon fim mafi kyaun hoto fim din Kakanda,
Sai gwarzon mai bada Umarni shima Kakanda, fim mafi kyawun tsara waje, fim ɗin Kakanda.

Wannan kyautuka ne suka mayar da fim ɗin Kakanda wanda ya fi samun kyautuka a wannan gasar.

By ukarofi