Ƙungiyar SWAN ta bada babbar lambar yabo ga wakilin Manhaja, Abdullah Tanko

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙungiyar marubuta labaran wassanni ta ƙasa (SWAN) ta bayar da mafi girman lambar yabo ga tsohon shugaban ƙungiyar reshen jihar Katsina kuma Wakilin Blueprint Manhaja, Kwamred Abdullah Mohammed Tanko.

Sakatariyar ƙungiyar ta ƙasa ce ta shirya bikin bayar da lambobin yabon a Abuja don girmama ‘yan jarida na ɓangaren wasanni waɗanda suka ba da gudummawa a lokuta daban-daban ga ci-gaban ƙungiyar.

Shugaban SWAN na Jihar Katsina, Kwamared Nasir Gide, wanda ya wakilci Abdullahi Tanko a bikin, ya miƙa masa lambar yabon ne a wani biki da ya gudana a Katsina.

Ya bayyana gudunmawar Kwamred Abdullahi Tanko ga aikin jarida na wasanni a matsayin abin yabo kuma abin koyi, musamman a lokacin da yake shugaban ƙungiyar SWAN ta jihar Katsina.

Ya tunatar da cewa a lokacin, ƙungiyar ta shaida manyan sauye-sauye waɗanda suka kara yawan mambobin kungiyar kuma suka zaburar da ‘yan jarida wajen shiga harkar wasanni da motsa jiki.

Ya kuma bayyana yadda Kwamred Abdullahi Tanko ya yi amfani da kafofin watsa labarai don ƙarfafa goyon baya ga ƙungiyar kwallon kafa ta Katsina United da ƙungiyoyin wasanni a sauran fannoni, da kuma ƙarfafa wa gwamnatin jihar gwiwa wajen farfaɗo da ayyukan wasanni daban-daban don lashe kofuna a gasar wasanni.

A nasa jawabin, shugaban Kungiyar ‘Yan Jaridar Wakila, reshen jihar Katsina, Kwamred Yusuf Ibrahim Jargaba, ya buƙace shi da ya cigaba da bada gudummawarsa ga cigaban ƙungiyar a jihar.

Da yake magana, Kwamred Abdullahi Mohammed Tanko ya bayyana godiyarsa ga sakatariyar SWAN ta ƙasa bisa karramawar da ta yi masa, wanda ya ce zai ƙarfafa masa gwiwa wajen cigaba da bada gudummawa ga ƙungiyar.

Ya kuma yi amfani da damar wajen kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta binciki ɓarna da satar manyan fitillu da kayan motsa jiki da sauran na’urorin da darajarsu ta kai miliyoyin Naira a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta rubanya kasafin da take ma bangaren wasanni tare da bada muhimmanci ga bangaren domin tallafawa matasa da kuma yin fice a gasar wasanni na ƙasa.

Lambar yabon mai taken ‘SWAN Fellowship Award (FSWAN)’ ita ce lambar yabo mafi girma a ƙungiyar ta SWAN.

Abdullahi, wanda wakilin jaridar Manhaja Blueprint Hausa ne a Katsina, ya shafe fiye da shekara 30 yana riƙe da ƙungiyar.

By Babaji