Boko Haram da ISWAP sun yi ba-takashi kan jagorancin Tafkin Chadi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yankin Tafkin Chadi na fuskantar sbaon rikici yayin da ƙungiyoyin ikirarin jihadi na Boko Haram da ISWAP suka yi artabu a tsakaninsu da nufin samun wajen zama a tsibirin ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa da ke jihar Borno a yankin.

Wani rahoto da Zagazola Makama, mai sharhi akan lamuran tsaro ya fitar a jiya Lahadi, ya ce al’amarin ya faru ne a ranakun 5 zuwa 8 ga watan Nuwamba, 2025 a yankunan Sahel na 1, Dogon Chuku, Mangari da yankunan ruwa na Tumbun Gini, Tumbun Shanu, Mangari da Dumba.

Rahoton ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram ƙarƙashin jagorancin kwamandojinsu Hassan Buduma da Mohd Hassan ne suka farmaki sansanonin ISWAP da wasu muggan makamai a yankin Tumbun Gini.

Daga baya sun sake sauya sheƙa inda suke nufi sansanonin ISWAP da ke yankin tafkin, lamarin da ya tilasta wa mayaƙan na ISWAP barin wajen tare da koma wa yankunan Ali Jillimari, Metele, Kangarwa da Gudumbali.

Zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a san adadin waɗanda suka rasa rayukansu ba, saidai binciken sojojin sashen leƙen asiri ya nuna cewa an gano gawarwaki masu yawa a saman ruwa yayin da aka kuma ga ramukan da aka binne wasu.

Har’ilayau, rahoton Makama ya nuna cewa, manufar Boko Haram ita ce korar ISWAP daga yankin Tafkin Chadi tare da karɓe iko da yankin, wanda ya haɗe ƙasashen Nijeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

By Babaji