
Tsararren jagoran ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta dakatar da shirin yanke hukunci kan tuhumomin ta’addanci akansa da Gwamnatin Tarayya ta gabatar.
Lauyoyin Kanu sun ce akwai muhimman batutuwa na doka da har yanzu ba a warware ba, don haka ba zai dace kotu ta yanke hukunci ba har sai an gama tantance waɗannan batutuwa.
Kanu ya bayyana cewa kotun ta ƙi amincewa ta tantance hujjojin da aka bayar akansa domin yanke ko sun inganta ta yadda za a hukunta shi akansu ko kuma ta soke su idan aka gano cewa ba gaskiya ba ne bayan gudanar da nazari akan su.
Haka kuma, ana cigaba da sauraron ƙarar da ta ja hankali a faɗin kasar, yayin da magoya bayan Kanu ke bukatar a sake shi nan take daga tsare shi da ake cigaba da yi tun daga shekarar 2021.
