
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta karɓi kimanin ƴan Nijeriya su guda 180 da suka dawo daga ƙasar Libiya.
An siffanta mutanen da marasa galihu da suka maƙale a ƙasar bayan kwaso su a ranar Talatar da ta gabata.
NEMA ta ce mutanen sun sauka ne a Filin jinginen sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.
Daga cikinsu, akwai maza manya 45, da mata manya 102, da yara maza shida, da kuma yara mata 13, sai kuma jarirai maza da mata guda bakwai-bakwai.
A sanarwar da NEMA ta fitar, ta ƙara da cewa 46 daga cikinsu ba su da lafiya, lamarin da ya sa aka tafi da su wurin kula da lafiyarsu.
Ƙungiyar kula da harkokin ‘yan gudun hijira ta duniya International Organization for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin jiglar bisa haɗin-gwiwar hukumomin Nijeriya.
