Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jami’ar All Progressive Congress reshen Jihar Zamfara ta koka kan abin da ta bayyana da zargin shirin da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP ke yi na kawo ruɗani da kuma haifar da rikici a lokacin ziyarar ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle zuwa jihar.
Jam’iyyar ta sanar da cewa Ministan zai kawo ziyara ta kwanaki uku a jihar.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Yusuf Idris ya yi wannan tsokaci a wani taron manema labarai kafin ziyarar Minista Matawalle da aka shirya yi gobe.
“Dangane da rahoton da jam’iyyar APC ta samu, gwamnatin PDP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki nauyin ‘yan dabar siyasa domin su Kai farmaki ga mambobin mu da magoya bayanmu a lokacin ziyarar da aka tsara za ta kasance gobe.” Yusuf ya ce.
Ya kuma zargi gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal da bada umarni ga dukkan membobin kungiyar NURTW ta ƙasa da kada su bari a ɗauki ‘yan Jam’iyyar APC aiki domin kai magoya bayansu Wajen tarbar ministan.
Jam’iyyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen kare ‘yan jam’iyyar ta APC da magoya bayanta a lokacin ziyarar.
Yusuf ya bayyana cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da bin doka, yana mai kira ga dukkan ‘yan jam’iyyar da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu kuma su bi doka a lokacin ziyarar da kuma bayan ziyarar.
