
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya ce ma’aikatarsa na bincke akan jayayyar da aka samu tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da kuma wani hafsan sojin ruwa mai suna A. M. Yerima akan dambarwar ikon mallakar fili.
Badaru, a wani taron mana labarai a Abuja, ya ce rundunar sojin Nijeriya ba za ta taɓa juya baya ga duk wani jami’inta da ke gudanar da aikinsa bisa doka ba.
Ya sanar da hakan ne bayan jayayyar da aka yi tsakanin Nyesom Wike da jami’in sojin ruwa, A.M Yerima a jiya, Talata 11 ga Nuwamba, lamarin da ke cigaba da janyo hankalin al’umma.
“Muna nazari kan batun, kuma muna bayar da tabbacin cewa za mu kare duk wani jami’inmu da ke kan aikinsa bisa doka. Ba za mu taɓa bari wani abu ya faru da jami’inmu da ke gudanar da aikinsa yadda doka ta yi tanadi ba.”
A ranar Talata bidiyon jayayya tsakanin Ministan na birnin Abuja da wani matashin hafsan sojin ruwa ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ministan ya yi jayayya da sojan a kan wani fili da ake ginawa mallakin tsohon babban hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo.
Wike da tawagrasa sun ziyarci wajen da filin yake tare da neman a nuna masu takardun izinin mallakar filin, inda ministan ya haƙiƙance cewa ba a cika ƙa’ida ba wajen mallakar takardun filin.
Sannan, sojojin kuma sun hana ministan shiga filin, lamarin da ya fusata shi har ta kai ga musayar kalamai a tsakanin ɓangarorin biyu.
