
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta ce ta yi nasarar gano mota ƙirar Toyota Hilux da aka sace daga ofishin mataimakin gwamnan jihar.
A cewar rahoton da ofishin mataimakin gwamnan ya samu daga ƴan sanda, an gano motar ne da safiyar Laraba bayan bincike mai zurfi na haɗin-gwiwa tsakanin jami’an tsaro.
Haka kuma, an kama wanda ake zargi da satar motar, wanda aka ce direba ne a gidan gwamnatin jihar.
A yanzu haka yana hannun ƴan sanda inda ake cigaba da gudanar da bincike akansa domin gano ainihin yadda al’amarin yake.
Ofishin mataimakin gwamnan ya jinjina wa yadda rundunar ƴan sanda ta gaggauta ɗaukar mataki da kuma ƙwararrun hanyoyin da ta bi wajen gano motar.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar, ofishin ya lamarin q matsayin cin amana daga ɓangaren wanda aka kama.
