
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris ya ce Shugaba Bola Tinubu na aiki tuƙuru wajen ganin ya sanya ƴancin yaɗa labarai a matsayin ginshiƙi daga cikin ginshiƙan samun nasarori a Nijeriya.
Mohammed Idris ya bayyana haka ne a Abuja, yayin babban taron Editocin Nijeriya, inda ya ce babu wani gidan jarida da ke fuskantar barazana ko aka rufe shi a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba harkar goyan baya da tallafa mata wajen ganin an yi nasara a ayyukansu duba da yadda suke aiki tuƙuru wajen isar wa al’umma saƙonni da kyawawan manufofin gwamnati.
Ya bayyana cewa, yana da muhimmanci al’umma su sani cewa babu koda ɗaya daga cikin gidajen rediyo da talabijin guda sama da 1,000 da ke da lasisi a Nijeriya ke fuskantar wata barazana daga gwamnati.
Ministan ya ƙara da cewa, duniya ma ta shaida ƙoƙarin Tinubu na kula da ƴancin harkokin jarida a Nijeriya, wanda hakan ya sa ƙasar ta jagorantar ƴancin harkar jarida ta ƙasa-da-ƙasa da Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai.
A cewarsa, harkar yaɗa labarai na samun ci-gaba a Nijeriya ta lamuran yaɗa labarai wajen ilimantarwa da faɗakat da al’umma, lamarin da ya sa kima da darajarsu ke ƙara yin sama a mataki na duniya.
Kazalika, ya kiyayi editoci da su riƙa kallon kansu a matsayin waɗanda ke da muhimmiyar rawar takawa a ci-gaban ƙasa.
