Daga JOHN D WADA a Keffi
Shugaban Cocin Evangelical Reformed Church of Christ da aka fi sani da (ERCC) a turance Rabaran Dave Denji, ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mambobin cocin gaba ɗaya domin samun cigaba da bunƙasar cocin.
Ya bayyana hakan ne a jawabin sa a wajen wani gagarumin bikin cika shekaru 10 na ERCC solution centre dake garin Masaka a ƙaramar hukumar Karu Jihar Nasarawa ranar Lahadi.
Wakilin mu ya ruwaito cewa anyi bikin ne domin tunawa da shekaru 10 da kafa majami’ar inda mambobin cocin da baƙi suka fito fili da tufafin su masu kyau suna bayyana farin cikin su tare.
Har ila yau, an samu halartar manyan baƙi a wajen babban bikin mai ɗinbin tarihi da suka haɗa da Dr. Joseph Haruna Kigbu da Dr. Emmanuel Akolo, da sauran manyan mutane.
Shugaban ERCC ɗin Rabaran Dave Denji, wanda wakilin shugaban taron Rev. Stephen Shammah ya wakilta, ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin mambobin cocin yana da muhimmanci.
Ya kuma ƙara da cewa duk wanda ya samu damar shiga cikin ayyukan cocin, to ya kamata ya yi duk abin da zai yi domin cocin ya cigaba.
Ya taya ERCC solution centre ɗin munar ganin ranar cika shekaru 10 inda ya kuma yaba wa shugabanni da duka mambobin cocin baki ɗaya musamman dangane da aiki tuƙuru da kuma sadaukarwa da suke yi har zuwa ranar, sannan ya buƙace su da su daure da hakan.
A nasa ɓangaren Dr. Joseph Haruna Kigbu, wanda ya kasance shugaban taron ya bayyana godiyarsa ga mambobin cocin saboda girmamawa da suka yi masa tare da ɗaukar alƙawarin tallafawa cocin a duka matakai da suka dace inda ya kuma ƙara da cewa bautawa Ubangiji shine hanya ɗaya tilo na samun nasarar rayuwa a nan duniya da ma ranar ƙiyama.
Haka shima a nasa ɓangaren shugaban kwamitin bikin tunawa da shekaru 10 ɗin wato Elder Allan Tsaku, ya bayyana cewa cocin an kafa shi ne a shekarar 2015 ba tare da wata manhaja ba, amma duk da haka cocin ya samu ci gaba mai ban mamaki a matakai daban daban da hakan ne ma yasa suka ga yadace a gudanar da taron don nuna farin ciki da godiyar Allah.
Mahukuntan cocin sun kuma karrama wasu manyan mutane da lambobin yabo na musamman kafin ainihin ranar bikin kenan wato a daren ranar Asabar inda aka kuma yi ciye-ciye da lashe-lashe a yayin liyafar daren.
Tun farko a jawabin shugaban cocin ERCC solution centre da ta cika shekaru 10 ɗin. Rabaran Johnson Abaka ya buƙaci mahalarta su bayar da kyaututtukan su da alƙawuran da suka yi domin kammala aikin cocin wadda yace a yanzu haka ake bukatar naira miliyan 20 don kammalawa da sauran ayyuka.
Rabaran Johnson Abaka ya kuma bayyana godiyarsa ga Ubangiji da kuma soyayyar sa duk tsawon tafiyar cocin.
Ya kuma jaddada muhimmancin tsayawa tare a kan dutse mai tsarki na Kristi da hakan nema yace musabbabin ɗinbin nasarori da cocin ta cimma cikin waɗannan shekaru 10 masu albarka.
