
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Lahadi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar da sabon ƙididdiga na waɗanda suka yi rajistar zaɓe a faɗin Nijeriya waɗanda adadinsu ya kai 2,316,232, sannan kuma hakan ya nuna Jihar Osun ita ce akan gaba da mafi yawan mutane.
INEC ta ce hakan wani ɓangare ne na kula da tsare gaskiya da adalci a yayin gudanar da al’amarin, wanda yanzu an kammala mako na 12 da farawa.
A cewar hukumar, Osun tana da jimillar mutane 185,089 da suka kammala rajista, sai Imo mai mutane 143,386. Ita kuwa Jihar Kano, wadda ke mataki na uku ta samu mutane 132,290, yayin da Sakkwato kuma take da mutane 123,320.
Legas ce ke biye da su da mutane 109,693; sai birnin tarayya Abuja mai mutane 106,855 da Borno mai 106,376.
Jihar Kogi tana da 91,573; Jigawa, 88,209; Zamfara, 84,268; da Katsina, 80,425.
Sai kuma Kaduna, 78,282; Kebbi 74,159; Delta, 72,311; Ogun, 71,091; Neja, 69,739; Akwa Ibom, 65,446 da Oyo, 64,561.
Sauran sun haɗa da Adamawa mai guda 49,853; Kwara, 47,241; Yobe, 46,986; sai Ribas mai 57,251.
Benuwai tana da 42,557, Bayelsa 38,627, Bauchi 36,166; Ekiti 32,096; Gombe 31,542, da kuma Nasarawa 30,348.
