Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da sabuwar Majalisar Sarakunan Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da sauran sarakuna uku na Gaya, Ƙaraye da Rano a matsayin mambobi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Kano ranar Litinin.
Ƙaddamarwar ta zama sabon babi a tarihin masarautar Kano, bayan rattaɓa hannu kan dokar Kano Emirates Council Law (Repeal Bill) 2024, wacce ta rushe masarautu biyar da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙiro.
A yayin taron da aka gudanar a Coronation Hall na Gidan Gwamnati, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce kafa majalisar na da nufin ba wa tsarin gargajiya damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba a jihar.
Gwamnan ya bayyana tsarin masarautun gargajiya a matsayin ginshiƙin tarihi, mai kula da ɗabi’u da al’adun mutane, kuma mai taka muhimmiyar rawa wajen zaman lafiya da tafiyar da mulki.
“Ƙaddamar da wannan Majalisar Sarakuna a yau na sake tabbatar da ƙudurin gwamnatarmu na kare tsarin al’adun Kano, ƙarfafa nagartaccen mulki da kuma zurfafa haɗin kai tsakanin gwamnati da masarautun,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa: “Mun hango wannan majalisa a matsayin wuri guda da sarakunanmu za su riƙa taruwa, tattaunawa, tare da ba da shawarwari masu inganci kan al’amuran da suka shafi jin daɗin al’ummar jihar.”
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya nuna kyakkyawar fatan cewa majalisar, idan ta fara aiki, za ta taka muhimmiyar rawa wajen cigaban jihar.
A nasa ɓangaren mai ba da shawara kan harkokin masarauta, Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, ya gabatar da cikakken bayani kan tarihin masarautar Kano da alaƙarta da masarautun Rano, Gaya da Ƙaraye.
Farfesa Naniya ya ce Gwamnan ya dawo da tarihin sama da shekaru 700, lokacin da sarakunan Kano ke ƙarƙashin shugabancin sarki guda domin ci gaban al’umma.
Sarkin Kano kuma shugaban Majalisar, Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda ya yi magana a madadin sauran sarakuna uku, ya ce dawo da majalisar a wannan lokaci ya yi daidai da tarihi.
Sannan ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gagarumar nasarar da yake samu a faɗin jihar, tare da tabbatar da cewa masarautu za su ba da dukkan goyon baya wajen cigaban Kano.
