Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka ƙaddamar da naɗin Alhaji Muhammadu Sani ɗanjuma ɗakin Gari a matsayin sabon Sarkin Hausawan garin Epe bayan amincewar Majalisar Sarkin Hausawan Legas, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muhammadu Sani Kabiru, tare da goyon bayan Mai Martaba Sarkin Yarbawan Epe, Oba Kamaluddeen Animashawun. Taron ya gudana ne a harabar fadar sabon sarkin da ke Epe, kuma ya samu halartar sarakunan Hausawa daga sassa daban-daban na Legas, shugabannin al’umma, da ɗimbin jama’ar Hausawa mazauna yankin Epe da kewaye.
Kafin nadin rawanin sarauta, Sakataren fadar Sarkin Hausawan Legas ya gabatar da tarihin sabon sarkin, inda ya bayyana cewa Alhaji Muhammadu Sani Danjuma Dakin Gari asalin mutumin Aljannare a ɗakin Gari, ƙaramar Hukumar Suru ta Jihar Kebbi ne. Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a can gida, kafin daga bisani ya tunkari harkokin kasuwanci domin neman abin duniya. Ya fara ne da zama a Jihar Ondo, inda ya shafe shekaru yana gudanar da sana’ar gwagwan. Daga nan ya komo Legas ya zauna Idiyaroko, yana shigo da kaya daga ƙetare zuwa Nijeriya. Bayan dogon lokaci a cikin wannan sana’a, ya sake komawa Epe inda ya ci gaba da kasuwancinsa har ya jagoranci kungiyar masu sana’ar gwagwan a yankin.
A halin yanzu yana zaune a unguwar T-Junction a Epe, inda yake ci gaba da gudanar da kasuwancinsa cikin kwanciyar hankali da girmamawa daga al’umma. Wanda hakan ya ƙara tabbatar wa majalisa cewa cancantarsa ta jagoranci al’ummar Hausawa a Epe ta fito fili.
Bayan an karanta tarihin rayuwarsa, kwamitin nadin sarauta ya ɗaura masa rawanin sabon Sarkin Hausawan Epe cikin cikakken girmamawa. Da yake jawabi, Alhaji Muhammadu Sani ɗanjuma ɗakin Gari ya nuna matukar jin dadinsa da wannan girmamawa da akayi masa, inda ya mika godiya ga Mai Martaba Sarkin Hausawan Legas tare da dukkanin majalisar fadarsa, da kuma Sarkin Yarbawan Epe da majalisarsa, bisa amincewar da suka yi masa.
Ya bayyana cewa wannan sarauta nauyi ce mai girma, kuma ya yi alkawarin gudanar da cikakken shugabanci nagari wanda zai kare martabar Hausawa a yankin, tare da tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da mutunta juna tsakanin al’ummar Epe gaba daya. Ya kuma bukaci jama’a da su bashi goyon baya domin ya samu damar aiwatar da ayyukan da suka dace da matsayin da aka dora masa.
Naɗin sarautar Alhaji ɗanjuma ya ƙara shigar da al’ummar Hausawan Epe cikin sabon matakin ci gaba da haɗin kai, inda jama’a suka bayyana farin cikin su bisa samun shugaba mai naci, mutunci da kishi.
