An rufe makarantun kwana a Yobe kan rashin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ƙoƙarinta na ɗaukar matakan kariya game da al’amarin taɓarɓarewar tsaro, Gwamnatin Yobe ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana da ke sassan jihar.

Darakta Janar na harkokin yaɗa labaran Gwamna Mai Mala Buni, wato Mamman Mohammed ya sanar da haka a wata takarda, jiya Asabar.

Ya ce, gwamnati ta ɗauki matakin ne bayan ganawa tsakanin gwamnan da jagororin hukumomin tsaro a jihar.

A cewar sanarwar, Gwamna Buni shi ya jagoranci zaman, wanda aka yi nazari akan matsalolin tsaro da suka shafi sassan ƙasar a ƴan kwanakin nan.

Ya bayyana cewa, gwamnatin ta yi haka ne da nufin ɗaukar matakan kariya ga ɗalibai da makarantu.

A wani saƙon umarni da Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimin matakin ƙasa da na sakandare, Dakta Bukar Aji ya fitar, an umarci da a gaggauta rufe makarantun kwana har zuwa lokacin a za a samu sauƙin matsalolin rashin tsaro.

Kazalika, gwamnan ya kirayi al’umma da su riƙa yin addu’a ga shugabanci, hukumomin tsaro da samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji