Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗaliban masu karatun digiri kowane ya sami Naira 30000,sai masu karatun Diploma nan ma kowane ya sami tallafin Naira dubu 20,000.
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai kuma Dujiman Katsina Hon Abdullahi Aliyu Ahmed ya sanar da haka a wajen bikin raba tallafin karatun ga ɗaliban a garin Musawa.
Dujima wanda ya ke wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu a majalisar wakilai ya ce ya bada wannan tallafin ta hannun kwamitin harkokin ilmi da ya kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon mataimakin gwamnan jihar Alhaji Tukur Ahmed Jiƙamshi.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa wannan ɗalibai da ke karatu a mayan jami’o’i, kwalejojin ilimi da na kimiyya da fasaha an zaƙulo su a sassan kananan hukumomin “sai da kwamitin ya tantance su kafin da suka amfana da tallafin,”Inji Dujima.
Ya ce ya zaɓi harkar ilimi a matsayin ƙudirin da ya fara sanyawa a gaba domin gina makomar matasa a yankin.
Yana mai cewa wannan tallafi zai taimaka wa ɗaliban da iyayensu masu ƙaramin ƙarfi don suma suyi gogayya da ya’yan masu hali a wajan samar da ingantaccen ilimi.
Ɗan majalisar ya jaddada ƙudirin sa na maida hankali wajen tabbatar da ganin matasan yankin sun amfani da shirin a kan harka ilimi,samar da aikin yi, tallafawa sana’o’in hannu, harkokin noma da sauran su.
Ya sanar da cewa nan bada jimawa ba zai raba takardar aikin gwamnati ga matasa 420 da suka fito daga mazaɓar sa ta Musawa da Matazu.
A baya ma sai da ya samar da irin waɗannan takardun guraben aikin gwamnati guda 181 a ma’aikatun gwamnatin tarayya da suka haɗa da Asibitin koyarwa da babban asibitin gwamnatin tarayya.
Sauran ma’aikatun akwai ofishin kashe gobara, hukumar yan sanda,sojoji, hukumar shige da fice, civil defence da sauran su.
Ya ce wannan guraben aiki gudunmawar sa ne wajen magance rashin aikin yi.
Dujima ya sanar da raba baburan hawa guda 500 da zai rabawa matasa ko wannan ya rage zaman banza.
Ya bayyana cewa nan bada jimawa ba za ayi bikin raba baburan hawan.
A jawabinsa shugaban ƙaramar hukumar Musawa,Hon Aliyu Idris Gingin ya bayyana yunƙurin ɗan majalisar akan inganta ilmi a yankin da ya ce wannan abin alheri na ɗaya daga romon dimokuraɗiyya.
Gingin ya bayyana cewa wannan tallafi da Dujima ya ƙaddamar yazo daidai da kundin tsarin ilimi na gwamna Dikko Raɗɗa.
