‘Yan bindiga na shirya wa harin Amurka wajen amfani da yara a matsayin kariya, inji Jerry Gana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana ya koka game da al’amarin garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a arewacin Nijeriya, yana mai gargaɗin ta yiwu ƴan bindiga suna yin haka ne domin amfani da ƴan makaranta da ƙauyawa a matsayin kariya ga harin da Amurka ka iya kawo wa Nijeriya.

A jiya Asabar Farfesan ya bayyana haka a wani taro na musamman don karrama shugaban Hukumar Kwastom (NCS) Bashir Adewal Adeniyi, wanda ya zama sabon shugaban ƙungiyar jami’an Kwastom ta Duniya (WCO).

A cewar Gana bayanan sirri da salon hare-haren ƴan kwanakin nan sun nuna cewa ƙungiyoyin ƴan ta’adda na yin haka ne bisa la’akari da kalaman Shugaba Donald Trump na Amurka cewa zai ɗauki matakin soja akan Nijeriya bisa zargin kisan Kiristoci a ƙasar.

Tsohon ministan ya ce ya samu kira sa’o’i kaɗan gabanin faruwar al’amarin da ke nuni da haka: “akwai yiwuwar ƴan bindiga su fara garkuwa da dandazon mutane, musamman matasa domin kariya ga fakon su.”

Ya bayyana cewa, hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa wasu yankuna da garkuwa da mutane musamman ɗalibai a makarantu, kariya ne ga harin ka iya zuwa musu ta sama.

Kalama nasa na zuwa ne ƙasa da mama guda da aka yi garkuwa da ɗalibai mata a makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga da ke Jihar Kebbi da kuma wasu ɗalibai da malamai su guda 315da aka sace a St. Mary’s Private School, Papiri a Agwara, Jihar Neja.

By Babaji