
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojojin ƙasa ta ce ta fara gudanar da binciken cikin gida game da zargin cewa sojojin da aka tura aiki a makarantar mata da aka sace ɗalibai 25 sun janye gabannin ƴan bindiga su isa garin, wato Maga a jihar Kebbi.
A yau Lahadi Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta sanar da matakin binciken biyo bayan cecekucen al’umma game da al’amarin duk da cewa bayanan sirri sun nuna cewa makarantu sune abin hari ga ƴan ta’adda.
A sanarwar da Daraktan Hulɗa da jama’a na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, Hedikwatar ta ce matakin zai taimaka wajen nazari akan salon tura jami’ai wurin aikin, matakan gudanarwa da aka bi da salon kula da bayanan sirri na yankin gabanin garkuwar.
Haka kuma hedikwatar na tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa dakarun tsaro suna cigaba ƙoƙarin ganin an ceto ɗaliban a jihohin Kebbi da Neja.
A wani labarin kuwa, Gwamna Nasir Idris ya bayyana kaɗuwarsa game da ayyukan sojoji a Maga, inda zarge su da barin yankin sa’o’i da faruwar al’amarin.
Haka kuma, ya ce sai da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sanar da saƙon bayanan sirri da ke gargaɗi akan yiwuwar faruwar harin.
