Gwamnatin Katsina ta biya Naira biliyan 23 kuɗin fansho da giratuti ga tsoffin ma’aikata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A shekarar 2019 zuwa 2023 gwamnatin Jihar Katsina ta biya Naira biliyan 23 ga ma’aikatan da suka ajiye aiki a matsayin haƙƙoƙin su na ajiye aiki.

Shugaban kwamitin tsara Sabon tsarin fansho a jihar Malam Farouk Aminu ya faɗi haka a wata ganawa da manema labarai, ya ce yanzu haka Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da fidda kudi Naira biliyan 20 domin biyan fansho da giratuti na ma’aikatan da suka ajiye aiki a shekarar 2023 zuwa 2025.

Haka kuma shugaban kwamitin ya bayyana cewa Gwamna Dikko Raɗɗa a ƙoƙarin sa na inganta rayuwar ma’aikatan da suka ajiye aiki ya ƙara kuɗin fansho daga mai ƙarancin Naira dubu biyar zuwa dubu 10.

Malam Farouk wanda yayi cikakken bayani kan sabon tsarin fansho inda ya ce wannan tsarin bai shafi ma’aikacin da zai ajiye aiki nan da shekara biyar masu zuwa.

Ya ce sabon tsarin fansho ya tanadi cire kaso bakwai bisa ɗari na albashin ma’aikaci,ita kuma gwamnatin jihar ta zuba kaso 13 bisa ɗari a duk wata har zuwa lokacin da zasu ajiye aiki.

Ya kuma tabbatar wa ma’aikatan jihar da kada su ji fargaban komai game da sabon tsarin fansho domin babu abinda zai canza dangane da adadin kuɗin da ake biyan yan fansho da na sabon tsarin.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa gwamnati jihar ta ƙirƙiro tsarin inshoran lafiya da tsarin nan na sai da masu da kayan masarufi bisa farashi mai rangwame.

Ya sanar da cewa gwamnati na nan za ta fito da tsari na da zarar ma’aikaci ya ajiye aiki a biya shi haƙƙoƙin sa nan take.

By ukarofi