DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed bisa kalaman tunzura

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, wanda tsohon abokin tafiyar Peter Obi ne a zaɓen 2023.

Baba-Ahmed, wanda kuma shi ya samar da Jami’ar Baze da ke Abuja, a cewar wata majiyar tsaro, an gayyace shi ne a jiya Juma’a da dare bisa zargin sa da yin waɗansu kalamai na tunzura jama’a akan Nijeriya.

An gano cewa DSS tana sanya ido akan kalaman Baba-Ahmed da aka baza su a kafafen watsa labarai musamman na ikirarin abinda ya kira da “rikicin dokokin ƙasa”.

Majiyar ta ce: “A kwanaki kaɗan da suka gabata, an ga Baba-Ahmed a wani gidan talabijin na ƙasa yana ɗora laifi akan shari’a da sojoji bisa ƙyale rantsar da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.”

Ta ƙara da cewa, Baba-Ahmed ya ce “rantsar da Tinubu shi ne ya ba sojoji damar kallon ƙwayar idonku su kira ku da wawaye”, wato ‘bloody fools’.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar ta ɗauki kalaman nasa a matsayin ababen da ka iya haddasa fitina musamman duba da yadda harkar siyasar ƙasar ke cikin hali na ƙarfin adawa.

Saidai, zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, DSS ba ta fitar da wani saƙo na musamman akan al’amarin ba.

By Babaji