Ɗaliban Sautus Sunnah 85 sun haddace Alqur’ani a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Makarantar Sautus Sunnah dake cikin birnin Katsina, sun shirya walimar haddar Alqur’ani Maigirma ga ɗalibai 85, don ƙarfafa ma ɗaliban da kuma ci gaba da yaɗa addinin Allah.

Taron wanda ya gudana a
cikin harabar makarantar dake bayan Water Boad Kofar Ƙaura, ya tara jama’a daban-daban don taya murna.

Ɗaliban Maza da Mata su 85 ne suka haddace Alqur’ani Maigirma a makarantar.

Da yake jawabi lokacin walimar, shugaban makarantar Malam Aminu Yakubu Musa PhD, ya bayyana jin daɗin sa kan wannan rana da kuma halartar taron wanda shi ne na farko da makarantar ta taɓa shirya walima a bainar jama’a.

Ya kuma gode ma iyayen ɗaliban da suka basu goyan baya da kuma ƙarfafa ma yaran su gwiwa na tabbatar da neman ilimin addini Islama.

Shi ma a jawabin sa, Sheikh Yakubu Musa Hassan, wanda ya assasa makarantar tun da farko, ya jinjina ma malaman makarantar na bada ilimi ingantacce da tarbiyya ga ɗaliban, ya tabbatar da cewa, ba za su iya biyan irin ɗawainiyar da Malaman ke ga ɗaliban su ba kan bada ilimin a wajen su.

Ya kuma ja kunnen ɗaliban da su yi amfani da ilimin da aka ba su don koyar da wasun su, domin haka zai ƙara yawaitar ilimi ga al’ummar yankunan.

Su ma iyayen yara, sun yi godiya ga malaman kan ba yaran su ilimi ingantacce, wanda zai amfane su duniya da lahíra.

By ukarofi