
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa Gwabin a matsayin sabon Ministan Tsaro.
Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a yau Talata.
Onanuga ya ce, a wata wasiƙa zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya miƙa sunan tsohon Babban Hafsan Tsaron na Nijeriya (CDS) a matsayin wanda zai gaji Alhaji Mohammed Badaru a muƙamin, wanda ya yi murabus a jiya Litinin.
Janar Musa mai shekaru 58, ya riƙe muƙamin CDS daga shekarar 2023 zuwa watan Oktoban 2025.
Ya kuma taɓa samun kyautar gwarzon soja na Colin Powell a shekarar 2012.
An haifi Janar Musa ne a shekarar 1967 a Sakkwato, inda a nan ya yi makarantun firamare da sakandare kana daga bisani ya cigaba da karatu a Kwalejin Ƙara karatu ta Zariya.
Ya kammala a 1986 sannan ya samu shiga makarantar sojoji ta Nigeria Defence Academy a shekarar, inda ya samu digirin farko a 1991.
