Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu na ganawar sirri da jagororin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu yana halin ganawa da jagororin hukumomin tsaron Nijeriya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Olufemi Oluyede ne ya jagoranci tawagar a fadar.

Sauran waɗanda suka samu halartar zaman sun haɗa da Shugaban sojojin ƙasa (COAS), Lt. Janar W. Shaibu; Shugaban Sojin Sama, CAS, Air Marshal Sunday Aneke; da Shugaban Sojin Ruwa, CNS, Vice Admiral I. Abbas.

Haka kuma, akwai shugaban sashen leƙen asiri, CDI, Lt. Janar Emmanuel Undiandeye; Shugaban DSS, Adeola Ajayi, da Sufeto Janar na ƴan sanda, IGP, Kayode Egbetokun.

Amma ba a samu jin ainihin maƙasudi zaman ba, wanda wasu ke ganin ana yi ne bisa la’akari da taɓarɓarewar tsaro a sassan ƙasar.

A yammacin jiya Litinin ne Ministan Ilimi, Badaru Abubakar ya yi murabus daga muƙaminsa, yayin da a yau Shugaba Tinubu ya sanar da bada sunan tsohon babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da shi a muƙamin.

By Babaji