Uwargidan Gwamnan Zamfara ta raba tallafin Kirsimeti ga mata Kiristoci

Spread the love

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau

Matar gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta raba tallafin jin ƙai ga mata Kiristoci da aka zaɓo daga ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da ƙungiyoyin ƙwadago da kuma hukumomin tsaro domin su yi bikin Kirsimeti cikin sauƙi.

An gudanar da bikin raba tallafin a gidan gwamnati, da ke Gusau babban birnin jihar a yau Talata.

Da ta ke jawabi a wurin taron, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yaba da irin goyon bayan da Kiristoci masu aminci suke bai wa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal.

Ta lura cewa irin wannan haɗin kai da goyon baya da suke bayarwa yana ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na inganta walwalar alummar jihar. Ta bayyana mata a matsayin ginshiƙai na zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

Uwargidan Gwamnan, ta bayyana cewa rawar da suke takawa wajen tsara iyalai da al’ummomi har yanzu abune mai muhimmanci.

“Ƙarfin Zamfara ya ta’allaƙa ne da juriya da jajircewar mata, su ne ginshiƙin al’ummarmu, kuma gudummawarku tana ci gaba da haifar da ci gaban jiharmu,” in ji ta.

Kayayyakin da aka raba wa waɗanda suka amfana, sun haɗa da buhunan shinkafa, tallafin kuɗi, taliya, sukari, man girki, da sauran muhimman kayayyaki da aka samar don sauƙaƙa masu a lokacin bukukuwan kirsimeti ga iyalai a faɗin jihar Zamfara.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa waɗanda suka amfana sun fito ne daga ƙungiyoyi daban-daban, waɗanda suka haɗa da CAN, Yoruba, Igbo, Gidan Zala, waɗanda ba ‘yan ƙasa ba, Sojoji, Jami’an Shige da Fice, Kwastam, ‘Yan Sanda, NSCDC, DSS, NDLEA, hukumar kula da kurkuku, Zarota, Red Cross, Malamai, ma’aikatan jinya, likitoci, mata ‘yan kasuwa, matasa, Masu hidimar ƙasa, ‘yan leƙen asiri, masu sayar da kaya, ma’aikatan kashe gobara, bankuna, da sauransu.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa an tsara wannan tallafin ne don rage wa mata nauyin da ke kansu a lokacin bukukuwan Kirsimeti da kuma tabbatar da cewa sun yi bikin Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da mutunci.

Ta buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su raba kayan cikin adalci, tana mai jaddada cewa shirin yana inganta tausayi, haɗin kai, da walwala ga kowa.

“Ina addu’ar wannan shekarar ta 2026, za ta kawo zaman lafiya, albarka da wadata ga kowane gida. Muna fatan za mu ci gaba da aiki tare don gina jihar Zamfara don zaman lafiya da wadata ya ɗore,” in ji ta.

Uwargidan Gwamnan ta sake jaddada ƙudirin ta na tallafawa shirye-shiryen da za su ɗaukaka rayuwar mata, ƙarfafa iyalai, da kuma inganta ci gaban al’umma.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta kuma yaba wa shugabannin mata, jami’an gwamnati, da wakilan ƙungiyoyi bisa jajircewa da sadaukarwa don cigaban Jihar Zamfara.

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa wakilan wasu daga cikin waɗanda suka amfana, sun hada da Mrs. Martila Udowella ta ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Lolo Ugueze Theresa Obijiaku, matar Mai Martaba Sarkin Igbo ta Gusau da Mrs Esther Ariyo ta ƙungiyar matan Yorabawa.

Sun yabawa Matar Gwamnan Jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal bisa jajircewa da tausayawa ga Mata ba tare da nuna Wani banbancin ƙabila ko addini ba.

By ukarofi