Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gidauniyar Musa Adamu Gwagware network ta yi wannan kira ta hannun shugaban ta kwamred Mannir Suleiman a Katsina.
Ya ce wannan kira ya zama dole ganin yadda shara ya cunkushe a magudanan ruwa da ke cikin garin Funtua.
Kwamred Suleiman ya ce wannan lamari ba ƙaramin illa bana ga lafiya al’ummar yankin.
“Jibge shara a magudanan ruwa na iya kawo ambaliyar ruwa a lokacin damina dama cututtuka kamar su cutar Maleria da sauran su”Inji Mannir Suleiman.
Sai ya yi kira ga al’ummar da su sa ido sosai domin kare magudanan ruwa da ke harabar su ga ƙananan yara harda mayan mutane waɗanda maimakon su kai sharar inda ya dace sun gwammace su zuba a magudanan ruwa.
Shugaban gidauniyar ya yaba da gwamna Dikko Raɗɗa kan yadda yake ba harkar kiwon lafiya mahimmanci ta hanyar ɗaukaka ƙananan asibitoci zuwa manya da samar masu da na’urorin zamani na gwaji.
Haka kuma ya jinjina wa malam Dikko Raɗɗa kan ƙoƙarin da yake na ƙara yawan jami’an kiwon lafiya”A yanzu haka akwai kwamitin da ke tantance ɗaukar ma’aikatan kiwon lafiya da suke zagaye faɗin jihar domin tantancewa,”Inji kwamred Suleiman.
