Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu a daren Laraba bayan da ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Danjibga da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sakamakon wata gardama da ta taso kan yoghurt ɗin Naira dubu uku da ɗari biyar.
Bayanan harin sun fito ne ta hannun wani masani kan harkokin tsaro, Bakatsine, ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
A cewarsa, rikicin ya fara ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka shiga wani shago suka nemi ɗaukar yoghurt ɗin Rufaida ba tare da sun biya kuɗinsa ba.
Lokacin da mai shagon ya nace sai an biya kuɗin kayan, rahoton ya ce ’yan bindigar sun fusata, suka bar kayan a wurin suka fice. Sai dai ƙasa da awa guda bayan haka, sun sake dawowa cikin shirin yaƙi, ɗauke da muggan makamai.
“Jiya da yamma a unguwar Danjibga da ke Tsafe a Zamfara, wasu ’yan bindiga sun shiga wani shago suka yi yunƙurin ɗaukar yoghurt na N3,500 ba tare da biyan kuɗi ba. Lokacin da mai shagon ya dage sai an biya, suka fusata, suka bar kayan suka fice. ƙasa da awa guda bayan haka, suka dawo ɗauke da makamai, suka fara harbe-harbe, suka kashe mutane uku, suka razanar da mazauna yankin, sannan suka wawashe shagon,” inji Bakatsine.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da harin ba.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙaruwar ayyukan ’yan bindiga a jihohi da dama na Nijeriya da suka haɗa da Kaduna, Kwara, Kano, Kogi da Filato, inda ake yawan sace mutane domin neman kuɗin fansa.
A ranar Lahadi da ta gabata ma, wasu ’yan bindiga sun kai hari wani coci a Jihar Kogi yayin da ake tsaka da ibada, inda suka sace fasto da matarsa tare da wasu masu ibadar da ba a bayyana adadinsu ba.
