“Marubuta na ba da gudunmawa muhimmiya kuma mafi tsoka a fagen shirya fim”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A makon jiya mun kawo muku kashin farko na tattaunawar da muka yi da tsohon Shugaban ƙungiyar Marubuta ta ANA reshen Kano, masanin harkar jarida, da zayyanar taswirar gidaje da muhalli, Tijjani Muhammad Musa. Don haka yanzu sai ku gyara zama ku cigaba da jin wannan tattaunawa da suka yi da Abba Abubakar Yakubu, wacce ke cike da fasaha da ilimi, irin na gogaggun manazarta adabi.
MANHAJA: Gaya mana abin da ya ja hankalinka ga salon rubutun waƙe irin na Haiku?
ARC. TIJJANI: Rubuta Haiku da Turanci na fara, shi kuma sha’awa ce ta sa ni na soma rubuta ta. A cikin salon rubuta waƙoƙi da Turanci fiye da 168 kawo yanzu na so Haiku ne saboda gajartarta ga ta da sa zurfin tunani ban da bam mamakinta wato cikin kalmomi ƙalilan da jimlar gaɓoɓin su a lissafe guda goma sha bakwai ake son ka rubuta ta. Ta kuma ba da ma’ana mai ɗorewa.
To, da shike ina son yanko malmala daga zantukan mutane fasihai wato “ƙuote” kenan sai na ga kamanceceniyar hakan da Haiku. Malmala ɗaya rak daga tukunyar tuwon adabin ta wadatar a ci a ƙoshi. Wannan dalili shi ya sa na ɗauki salon rubuta Haiku da Turanci a cikin ire-iren waƙoƙin da nake rubutawa.
Ko za ka ilimantar da masu karatun mu da ba su san mene ne Haiku ba?
Haiku wata waƙa ce da ta samo asali ko tushe daga ƙasar Japan. Inda ake rubuta wakar a cikin layuka uku. A kowanne layi ana son samun gaɓoɓi kamar haka biyar ana farko. Na tsakiya kuma ana son a samu gaɓoɓi bakwai sai layin ƙarshe na ƙasa a samu gaɓoɓi biyar. Gaba ɗaya gaɓoɓi goma sha baƙwai kenan ake so a jumlace.
To, shi ma Hausa Haiku wani salon rubutun adabi ne da ake yin sa da harshen Hausa, inda ake zubin haruffan da kalmomin cikin layuka uku-uku bisa dokoki, ƙa’idoji da sharuɗɗan da ake rubuta Haiku na ainahi wanda ya fito daga Japan da su. Bambanci dai Haiku da Hausa ba waƙa ba ce ta Hausa illa kawai salon magana ne a rubuce a ɗabi’ance da Hausa. In da Haiku na Japan yake maida hankali kan rubuta shi bisa doron halittun Allah Ta’ala kamar su yanayi (sanyi, zafi, rana, iska, ruwa dds), tsirai, bishiyoyi, furanni, ƴaƴan itatuwa da makamantansu, shi Haiku da Hausa akan yi magana, hira, wa’azi, jan hankali, faɗakarwa, yabo, ba da labari, yin karin magana, habaici, zambo, zaurance, gugarzana da dai sauransu da shi.
Kuma Hausa Haiku kan zo ta sigar a yi shi a ɗaiɗaiku, kowanne baiti ya yi zaman kansa, ko a jero su ɗaya bayan ɗaya a jumlace kamar zubin carbi wanda kan kasance daga baituka biyar, abin da ya yi sama zuwa 10, 21, talatin, hamsin, ɗari, dubu, miliyan ko ma fiye. Sannan ba a damuwa da yi masa ƙafiya.
Abin nema a shimfidar Haiku da Hausa shi ne zancen da ka ke yi ya ba da ma’ana ya sa zurfin tunani ya nuna kaifin basira ya nuna balaga ya nuna fasihanci ya nuna marubucin Haiku da Hausa yana da rumbun kalmomi don zaɓin wacce ta dace da lissafin samun gaɓoɓin nan 17, sai kuma ya nuna ƙwarewa wajen iya zanta zance da dai sauransu.
A taiƙaice dai wannan shi ne ɗan taƙaitacce bayani akan ko mene ne Haiku. Sannan akwai wani shahararren marubucin adabi cikin harshen Turanci da Hausa da ya sawa Haiku da Hausa suna ƙumbula.
Ba da jimawa ba ka fitar da wani littafin waƙe da ka wallafa da salon Haiku, game da sunayen Allah, me ya ƙarfafa maka gwiwar yin haka?
Wannan littafi mai suna ‘Sunayen Allah 99’ – Hausa Haiku na wallafa shi ne a farkon wannan shekara ta 2025 kuma shi ne littafi na farko a wannan sabon salon na rubutun adabin Hausa. Hakazalika shi ne littafina na farko a harshen Hausa.
Sannan kuma shi ne littafin da ke tafe da fassarar abin da ya ƙunsa cikin manyan harsuna uku da ke kan gaba da duniya take mu’ammala da su wajen gudanar da harkokinta wato Turanci da Hausa da kuma Larabci.
Abin da ya sa ni wallafa littafin shi ne in yi wa Ubangiji Allah (SWT) godiya ba kawai da baka ko a zuci ba a’a in yi masa hidima da arziƙin da Ya ba ni ta fannoni daban-daban kamar su ji da gani da fahimta da iya fassara daga harshe zuwa harshe kamar harshen Hausa da Turanci. Ga iya rubuta waƙe cikin harshen Nasara da na Hausa.
Baya ga wannan akwai ilimin zamani da na Islama da Ya huwace min. Sai kuma Ya yassare min iya rubuta waƙar Haiku da Turanci daga bisani Ya yardar min ƙirƙiro da iya rubuta Haikun da harshen Hausa.
Sai kuma Ya ba ni damar gabatar da Hausa Haiku ga duniyar marubuta da makaranta da manazarta da wasu ma’abota hulɗa da adabin Hausa ciki da wajen ƙasar Hausa ta fasahar yanar gizo wato intanet kenan da kuma dandalolin sada zumunta wato soshal midiya. Kuma da yawa an yi lale marhabun da wazuwar wannan sabon salo na rubutun waƙa a adabin Hausa. To, ganin haka ya sa na ga dacewar a wallafa littafi a kan samuwar Haiku da Hausa.
Daga cikin abin da suka ƙarfafa min gwiwar wallafa littafin shi ne irin musayar yawu da aka riƙa yi tsakanin masoya da saɓanin haka, wanda ke nuna karɓuwar wannan sabon abu cikin duniyar adabin Hausa. In da aka samu manyan malamai na harsuna a jami’o’i wasun su ma farfesoshi ne, wasu daraktoci, wasu kuma masu digiri da digirgir da yawa ban da wasu ƙwararru a harshen Hausa da suka nuna farin cikinsu da sha’awar karɓarta har suka gwada rubuta ta. To, gaskiya wannan ne kaɗan daga cikin dalilaina na samun karsashi da ƙwarin gwiwar buga wannan littafi na Hausa Haiku.
Yaya za a yi wannan salon rubutun da ku ke yi ya samu karɓuwa a wajen matasan Arewa da masu nazarin waƙoƙin Hausa?
To, Alhamdulillahi. Kawo yanzu dai babu abin da za mu ce sai hamdala. Don irin yadda cikin ɗan lokaci ƙanƙani Hausa Haiku ta karaɗe duniya, kowa har da sarakanmu na gargajiya waɗanda suka samu gamuwa da Haiku da Hausa sai tambaya suke shin mene ne Haikun nan ne, don ba su san kalmar ba a Hausa. Yi musu gamsasshiyar bayani a rubuce da kuma ganin zubinta a rubuce musamman Haiku Mai Carbi ya sa da yawa mutane hankalinsu na kai kawo a sanin mene ne Haiku da Hausa.
Matasa kuwa ai ƙiris suke jira sabon abu ya fito a gurguje za ka ga sun karɓa. To, hakazalika Hausa Haiku kullum daɗa shiga zukatan matasa salon yake yi, don da yawa za ka ga suna ta ƙoƙarin koyonta don ko yanzu idan ka yi bincike a Google na Hausa Haiku sakamakon da za ka samu zai ba ka mamaki.
Mu dai maƙirƙiran Haiku da Hausa namu ba abin gaggawa ba ne. Sannu a hankali duniya za ta karɓi al’amarin ko ba a ƙasar Hausa kai tsaye ba a ɓangarori daban-daban na duniya in da za ka ga ana nazarinta a jami’o’in Turai da ma sauransu musamman a tsangayoyin karatun harshen Hausa. Ko da bayan ranmu ne hakan zai biyo baya da yardar Allah.
Lokacin da ka shugabanci ƙungiyar Marubuta ta ANA Kano, waɗanne sauye-sauye ku ka samar a harkar rubutu?
Lokacin da na shugabanci ANA Kano 2021 zuwa 23 mun kawo sauye-sauye a ƙungiya da dama inda muka dinga gayyatar masana adabin Turanci da Hausa suna halartar taronmu na duk ƙarshen wata suna yi wa mambobinmu bita, da yin taron ƙarawa juna ilimi. Mun kuma jawo mambobinmu da aka samu saɓani tsakaninsu duk sun kau da rashin fahimtar juna an haɗe kai guri guda.
Mun kuma nemin yin racist wa dukkan marubuta da mawallafa don samun wani kundin da kai tsaye za a ga mambobin ANA Kano manya da matasa na da da na yanzu. Mun fara amma ba mu Ida ba wa’adinmu ya cika.
Sannan mun dinga gudanar da Makon Adabi na Kano in da muke shirya gagarumin bikin marubuta wanda akan yi tsawon sati guda a yi. Sannan da Ramadan mun yi Shan Ruwan Marubuta ko Ruguntsumin Marubuta don taya juna murnar Sallah ƙarama ko Babba.
Akwai gasa tsakanin makarantu da muka shirya don zaƙulo matasan marubuta in da har daukan nauyin buga musu littafinsu na farko akan yi. Ga dai abubuwa nan da dama da muka yi.
Wacce alaƙa ce tsakanin ANA Kano da Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano?
Alaƙa ce mai kyaun gaske da ya kamata a ce akwai ta kuma ingantacciya. Ka san rubutu fa shi ne ƙashin bayan dukkan wasu finafinai ko ilimantarwa faɗakarwa wayarwa tunatarwa da uwa-uba nishaɗantarwa.
Marubuta suna ba da gudunmawa muhimmiya kuma mafi tsoka a fagen shirya fim kuma da basira ko fasaharsu ake ƙirƙirar dukkan wasu saƙonni da za a so a isar ga al’umma don sauya musu tunani akan komai.
A wasu kasashen fa gwamnati na ware wani kaso na ƙudin da za ta kashe a bajet a duk shekara don a shirya mata fina-finai su isar da wasu buƙatu na hukumominta ga muanen gari ta sigar fim, amma a nan ne hakan har yanzu bai samu ba tukunna.
To, duk sanda haka za ta kasance marubuta ake nema su tsara labarin cike da fadakarwa ko ganarwa ko nusar da mutanen har su ji su gani su kuma ba tare da sun sani ba. Don sai marubuci ya ƙirƙiri yadda saƙon zai kasance a rubuce sannan su furodusa da darakta da jaruman fim ɗin za su san mene ne abin yi don tabbatar da cewa wannan majigin ya wanzu. Ka ga kenan babu fim.
In kuwa aka ce babu rubutaccen labari ai finafinai masu suna da cancantar a kira su fim da muka rubuta babu su. Dalilin da ya sa ke nan marubuta suke da tasiri da muhimmanci ga wannan hukuma.
Na ji ana ce maka Architect, wato masanin zana taswirar gidaje, me ya faɗo da kai fagen adabi?
Kamar yadda na yi bayani a baya ni horarren masani ne a fagen zana taswirar gidaje da muhalli don ɗan Adam ya gudanar da rayuwa ingantacciya a doron ƙasa. To amma ƙaddarar Allah SWT ta sa na zama “Architect” a turance ke nan.
Da nake matashi Turanci na so in karanta kamar yadda na yi bayani sai ta kasance san da na samu damar shiga Jami’ar Bayero a 1989 maimakon su ba ni English sai aka ba ni Economics wato karatun Tsumi da Tanadi. Ni kuwa na ce a’a.
Da ma da shike na iya ƴan zane-zane na nemi damar yin difuloma a fanin zana taswira a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano Polytechnic), kuma an ɗauke ni har mun fara karatun kafin takardar ɗaukata a BUK ta fito, sai kawai na ƙi barin Folin in koma Jami’ar.
To, ka ji yadda aka yi na zama architect kenan. Don da na gama karatun difulomar kai tsaye na wuce Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria na yi digiri a fannin na kuma kammala da digigir ɗina. Ta haka na samu zama horaren mai zana taswirar gidaje. Yadda kuma aka yi na tsinci kaina a fagen adabi bayanaina a baya sun gabatar da hakan.
Tun a tasowarka wanne aiki kaso a ce shi ka yi, kuma me ya kawo canjin da yanzu ka ke ciki?
Aikin Jarida na so in yi tun asali amma yanzu ma aikin sadarwa nake yi wato media serɓices, wanda ya ƙunshi dukkan abin da yake isar da saƙo.
Da kuwa na biyewa karatun da na yi da fari wato Architecture da yanzu na yi kace-kace a cikin harkar sarrafa gidaje zana su gina su sai da su da abubuwan da suke da dangantaka da su. Amma yanzu sadarwa ce babbar sana’ata sai kuma harkar tallata hajar manyan kamfanonin sadarwa irin su MTN da makamantan su. Alhamdulillah. Masha Allah.
Wacce karin magana ce take fi tasiri a rayuwarka?
Karin magana? Hmmm… ba lallai ba ne ta karɓu a wajen wasu ba, saboda ni na ƙirƙiro ta da kaina kuma nake amfani da ita wajen saitawa kai na rayuwa. Sai dai da Turanci na naƙalto ta, amma fassararta da Hausa ita ce,
Kowa na fafutukar ya rayu alhali mutuwa ce ƙarshensa.
Masha Allah. Mun gode ƙwarai da gaske.
Ni ma na gode.
