Gwamnatin Amurka na shirin aiwatar da sabon tsari da zai tilasta baƙi daga ƙasashen da ba sa buƙatar biza su miƙa cikakken tarihin kafafen sada zumunta na shekaru biyar kafin su samu shiga ƙasar.
Wannan sabon shiri, wanda aka buga a cikin Federal Register a ranar Talata, zai shafi ƙasashe 42 da ke cikin shirin Visa Waiver, ciki har da Birtaniya, Faransa, Ostiraliya da Japan. Yanzu haka, waɗannan baƙin na buƙatar ESTA kaɗai, wanda ba ya buƙatar bayanai masu zurfi.
Sai dai a sabon tsarin, gwamnati na neman maido da binciken asusun kafafen sada zumunta da dukkan ayyukansu na shekaru biyar a matsayin tilas, ba zaɓi ba.
Hukumomin Amurka sun bayyana cewa manufar ita ce tattara “muhimman bayanai” domin tsaurara tsaron ƙasa. Ana ba jama’a kwanaki 60 su yi sharhi kan wannan shiri kafin ya zama doka.
Wannan yunƙuri na ɗaya daga cikin tsauraran matakai kan hijira da tsaron iyaka da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ɗauka tun bayan dawowarsa ofis. A baya-bayan nan ma, an ƙara matsa lamba ta ayyukan ICE wajen cafke baki da ke karya dokoki.
A watan Yuni 2026, Amurka za ta karɓin miliyoyi baƙi domin gasar FIFA World Cup 2026 tare da Mexico da Canada. Masana na ganin sabbin dokokin na iya shafar yawan magoya bayan ƙwallon kafa da za su iya zuwa ƙasar.
