Dattawan Arewa sun buƙaci soke yarjejeniyar bayanan tara haraji tsakanin Nijeriya da Faransa

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Zauren Dattawan Arewacin Nijeriya da suka ƙunshi jihohi 19 na ɗaukacin jihohi talatin da shida jimlatan na ƙasar nan sun buƙaci Shugabsn ƙasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu daya gaggauta soke takardar yarjejjeniyar fahimtar juna da hukumomin tara kuɗaɗen haraji na ƙasashen biyu, “Federal Inland Revenue Service (FIRS) da  France’s Direction Générale des Finances (DGFiP) suka rattaba hannayen su, da gargaɗin cewa yarjejeniyar wata mummunar katoɓara ce ga ‘yancin tattalin Nijeriya, har ma da lamuran tsaronta.

A wata takardar jawabi da mai magana da yawun zauren dattawar, Abubakar Jika Jiddere ya fitar a birnin tarayya na Abuja a ranar Lahadi da ta gabata, dattawan arewan sun bayyana yarjejeniyar a matsayin wani makamin bauta na mulkin mallaka, suna masu zargin cewar, yarjejeniyar za ta bankaɗa ‘yan barandan duniya sirrace-sirracen haraji da bayanan tattalin arzikin ƙasar ta Nijeriya, da sunan haɗin kan fasaha.

Zauren Dattawan Arewan ya kuma yi gargaɗi da la’akarin cewa, wannan tsarin wani borin kai ne ya hau ta yadda tsarin tara kuɗaɗen harajin ƙasar zai kasance bankaɗadde maras sirri ga masu neman lakar cutar da ƙasa  ko yin banga-bangar bautarwa.

Har-ila yau, Dattawan sunyi yaƙinin cewa Nijeriya tana da wadatattun ƙwararru na hanyoyin fasaha daban-daban da za ta gudanar, tare da zamanantar da tsarin tara haraji, ba tare da sanya hannu ko tsoma bakin gwamnatin wata ƙasa ba.

Don haka suka ƙalubalanci bijiro yarjejeniyar a wannan lokaci da kan mage ya waye, da lamuran tsaron suka taɓarɓarce, fatara da muyata suka yi wa al’ummar ta katutu, darajar kuɗaɗen ke tauyewa, haɗi da zaman kashe wando da ya addabi al’umma, husasan a arewacin ƙasar.

Kamar yadda zauren dattawan ya ayyana, duk wani tsari da zai sanya wata ƙungiya ko gwamnatin ƙetare zuba idanu ko tsoma hannu a cikin lamuran haraji na Nijeriya ya yi shisshigi ko shiga sharo, haɗi da yin katsalandan wa ‘yancin ta na halattacciyar ƙasa.

Zauren dattawan sai ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi la’sakari da girmama ‘yancin sirrin ƙasa, haɗi da ɗorawa kamfanonin cikin gida a dukkan majiɓantan lamuran, tare da kafa ma’abutan dokoki da zasu yi kandagarki wa dukkan bayanai ko sirruka da suka jiɓanci tattalin arziki, husasan gabanin ƙaddamar da sabuwar hukumar tara haraji da aka tsara yi a watan Janairu, 2026.

Zauren, ya kuma zargi majalisar wakilai ta ƙasa dayin sakaci bisa ayyukan ta na bibiyar lamura da suka jiɓanci tarayyar ƙasar nan, yana mai gargaɗi yarjejjeniya makamanciyar wannan ba za a ƙulla taba ba tare da tuntuɓe-tuntuɓe ba, bajewa akan faifai da hangen ina ne aka dosa ba.

Dattawan na arewacin ƙasar nan don haka suka buƙaci gaggauta soke wannan yarjejeniya, daƙushe gudanar wa ko ta’amalin wata ƙasar waje kan duk wani lamari daya jiɓanci bayanan tattara kuɗaɗen harajin Nijeriya , tare da bukatar kira tayi wa kanta MAGANIN zawo.

Zauren ya kuma sha alwashin ƙalubalantar wannan wannan batu bisa tsarin doka daya kamata matuƙar gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da wannan batu ba.

Kawo wannan lokaci na buga labarin nan dai, walau fadar shugaban ƙasa, ko hukumar tattara kuɗaɗen harajin tarayyar Nijeriya , babu Wanda yace uffan kan wannan buƙatar ta Dattawan Aewacin Nijeriya.

By ukarofi