Sojojin Nijeriya sun cigaba da atisayen zuwa Portugal bayan Burkina Faso ta sake su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar Sojojin Sama na Nijeriya (NAF) ɗibar C-130 da aka tsare a Burkina Faso kuma aka sake su a ranar Alhamis, sun cigaba da gudanar da atisayen da suka ɗauko na zuwa ƙasar Portugal da jirgin da suka faro aikin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tawagar ta ƙunshi mutane 11 na sojoji, waɗanda suka nufi Portugal domin aikin kulawa da jirgin, wanda ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso sakamakon tsaikon gudanarwa.

Al’amarin ya faru ne a ranar 8 ga watan Disamba, 2025 a yankin Bobo-Dioulasso bayan lalacewar na’ura.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje na Nijeriya, Kimiebi Ebienfa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa jirgin da jama’ar ciki sun shirya zuwa Portugal ne gabanin al’amarin ya faru.

Ya ce, an sallame su daga Burkina Faso ne bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin tawagar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar da hukumomin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Ibrahim Traoré.

Daraktan watsa labarai na NAF, Ehimen Ejodame ya bayyana cewa jirgin ya sauka ne kusa da wani filin jiragen sama don kariya, bisa la’akari da tsare-tsaren sufurin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa.

By Babaji