
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyya mai mulki (APC) ta sanar da komawar Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang zuwa cikinta daga jam’iyyar PDP a jiya Alhamis.
Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yiltwatda, wanda shi ma ɗan jihar ne, ya sanar da haka yayin zaman jiga-jigan APC da aka gudanar jiya a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Farfesa Yiltwatda ya ce komawar Gwamna Mutfwang cikin APC ya nuna cewa baki ɗaya gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya sun zama ƴaƴan jam’iyyar.
A shekarar 2023 aka zaɓi Mutfwang a matsayin gwamnan jihar a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, inda shi ne wanda ya sauya sheƙa daga cikinta a baya-bayan nan zuwa APC.
Haka kuma, shugaban APCn ya ba dukkan mambobin jam’iyyar wa’adin 30 ga watan Junairun 2026 na su yi rajistar zama mambobi.
Ya bayyana cewa, samar da tsarin rajistar intanet ta ‘electronic membership registration system’ a matsayin abin da zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci tare kiyaye dokokin dimukraɗiyya a matakin cikin jam’iyya.
Daga cikin mahalarta taron akwai Mai Girma Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, jagorancin majalisar dokoki ta ƙasa da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Sannan, akwai gwamnonin jihohin Enugu, Peter Mba, Douye Diri na Bayelsa, Agbu Kefas na Taraba da Umo Enov na Akwa-Ibom da ya koma APC a kwanan nan.
Sauran sun haɗa da tsofaffin gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.


