NNPCL ya sake rage farashin fetur karo na uku a 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban ​Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya sake rage farashin litar man fetur a karo na uku cikin shekerar 2025.

​A cewar rahoton jaridar DAILY POST, wakilinta da ya zagaya gidajen mai a birnin Abuja ranar Alhamis, ya gano cewa NNPCL ta rage farashin man fetur zuwa N835 akan kowace lita a madadin N915 da ake sayerwa a baya.

​Hakan na nufin NNPCL ya yi wa kwastomominsa ragin farashin litar man da N80.

​Wannan ci-gaban ya biyo bayan matakin da sauran kamfanoni kamar masu hulɗa da Matatar Ɗangote irin su MRS, BOVAS, da AA Rano suka ɗauka na rage nasu farashin zuwa tsakanin N739 zuwa N865 akan kowace lita a a birnin tarayya Abuja.

​Rahotanni sun nuna cewa ragin farashin da NNPCL da sauran gidajen man suka yi ya zo ne bayan da matatar man Ɗangote da masu manyan ma’ajiyar mai suka rage farashin su zuwa tsakanin N699 da kuma N800.

​A baya-bayan nana ne NNPCL da sauran gidajen mai suka rage farashin man fetur da kaso mai girma akan yadda masu ababe hawa suke saye a baya.

By Babaji