Shugaban INEC ya gayyaci tsagin Turaki da Anyanwu kan rikicin PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Joash Amupitan, ta shiga tsakani akan rikicin shugabancin babbar jam’iyyar adawa, PDP, inda ta gayyaci ɓangarorin jam’iyyar biyu zuwa hedikwatarta da ke Abuja a ranar Juma’a.

Zaman ya haɗa ɓangaren da Tanimu Turaki ke jagoranta da kuma na Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa kiran ɓangarorin biyu ya zama wajibi saboda ta’azzarar rikicin cikin gida acikin jam’iyyar.

Bayan gabatar da jawabi, an shiga taron sirri domin samun sasanci tsakanin ɓangarorin da ke rikici, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ɓangarorin biyu sun gabatar da cikakkun bayanai game da lamarin kuma sun tabbatar da cewa yanzu haka batutuwa suna gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara.

A ƙarshe, Shugaban na INEC ya kammala da cewa an kira taron ne domin jin ta bakin ɓangarorin biyu, duk da cewa kwamitin ya san da shari’o’in da ke gaban Kotun Ɗaukaka Kara kuma hukuma tana jiran hukuncin ƙarshe na kotun kan al’amarin.

By Babaji